MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER36

MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER36
MUSAYAR ZUCIYA  CHAPTER 36 Gurin dayar nurse din ta karasa ta bawa baby boy din kafin ta dawo gurin ta kalli Sadeeq dake shafar kan INdo yana hura mata iskar bakinsa ganin bata bude ido ba.  “Angon karni leave us please kafin a gama shirya ta.” Da kyar Sadeeq ya iya yin magana ba tare da ya kalli nurse d’in ba yace. “Ki fara duba ta tukunna naga tayi haka bata kifta idanuwa sosai.”  “Ah karka damu wannan ba wani abu bane ba, kawai wahalar haihuwa ce kadan bamu guri tunda kaima ka bamu gudun mawa.”  Tashi Sadeeq yayi yana kallon INdo wadda idanunta ke a rufe sannan ya fita. Maman Sayyid makociyar su da suka zo tare ta kallesa tana zaune ta mike duk da cewar tajiyo kukan jariri tace.  “Malam Sadeeq yaya ita din?!”  “Sun ce zasu gyara sune but ni banga ita Aishan tana wani abu ba da zai nuna min cewar komai normal ba.”  “Insha Allah komai lafiya lau karka damu shi yasa banso ka shiga cikin ba naso ace kawai sai dai a kiraka ace kazo ka gansu.”  Numfashi yaja tare da yi mata godiya sannan ya wuce …