MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 35

MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 35
MUSAYAR ZUCIYA  CHAPTER 35 Shirin zuwa Sumaila kauyen sani suke farin ciki ya cika zuciyar INdo harta kasa boyewa, kallonta yayi bayan ta rufo dakinta ta juyo gashi cikinta ya fito yace.  “Cutie koma daki gaskiya mun fasa zuwa.”  Kirjin INdo ya shiga bugawa hankalinta duk yayi mugun tashi ta kallesa dan san tabbatar da maganarsa. Gani tayi yana dariya hakan yasa ta yin kansa zata dokesa yayi saurin guduwa cikin shagwabar da ta farayi wadda yanzu take neman zame mata jiki tace.  “Ka tayar min da hankali Allah ya dawo damu lafiya sai na rama.”  Fitowa suka yi suka shiga mota Sadeeq ya dauki hanya, wannan karan cikin hira suke kai daka gansu kasan masoyane sabanin lokacin da akace ya kaita garinsu ya dinga kumbura tamkar wanda aka sanyawa yeast. Cikin kwanciyar hankali suka shiga garin sumaila, suna zuwa kan kwanar da zasu shiga kauyen sani sadeeq ya kalleta yana murmushi yace.  “Cutie ga barkono da gyada bazaki siya bane?!”  Juyawa tayi tana kallon gurin kafin tace. “Eh wallahi kuwa, dan Allah …