MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 34
MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER34 —Tana fita napep ta tare ya kaita gidan su. Tana shiga ta fashe da kuka tare da fad’awa kan kujerar daya daga cikin falon. “Ke lafiya kuwa kamar wadda aka yiwa mutuwa?” Cewar yayan ta Shamsu yana kallonta, Fateema bata yi shiru ba tana ta kuka Shamsu ya tashi ya dinga mata fada yace idan baza tayi magana ba ta tashi ta koma inda ta fito. Mama ma kallonta take yi tanajiran jin abinda zata fad’a ranta cike da addu’ar Allah yasa ba tsakaninta bane da mijin. “Ke wallahi karki bari na tashi tsaye dan sai na fasa miki baki, aikin banza kawai kiyi magana shine zaki tsaya yiwa mutane kuka.” “Mama Sadeeq ya munafurce ni, Mama be taba gaya min matarsa Aisha nada ciki ba sai yau da muka gani gashi har ya fito. Wallahi bazan koma gidan saba yaje can su karata munafiki kawai, dama ance duk wacce ta dauki namiji uba toh lallai zata mutu ma…” Mtwww “Shut-up Fateema, bakida hankali ne? Toh sakinki kike so yayi?!” “Nidai kam bazan koma ba yaje can su karata.” “Toh idan ya sakek…