MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 32
MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 32 ‘Dan zamejikin ta tayi daga nasa ta kallesa, “shin da gaske ni yake so ko kuma cikin dake jikina? Anya malam Sadeeq kana sona kuwa? Amma zamu gani idan gaske ne.” “Kin yi shiru.” Dariya ce ta subuce mata ganin yadda yake kallonta tamkar wani mara lafiya, ganin tana dariya yasa shi jin wani farin ciki har cikin ransa ya kuma janyo ta cikin jikinsa yana shafarta, ba zai mata komai ba dan karma tayi tunanin dan hakan yake sonta yanzu gara ya daure ya hakura ana dauke ruwa kawai ya gudu gurin Fateema tunda Allah ya kasa ya bashi biyu. “Kana ganin yanzu babu abinda ya samu cikina?” “Insha Allahu karki damu, ko kinajin wani ciwon ne?” “A’ah banajin komai ni sai yunwa.” “Okay sorry bari ruwan naga ya fara d’an tsagaitawa sai na samo miki wani abun kici. Bafa ki bani amsa ta ba Aisha baki ce kin yadda zaki zauna dani ba.” Dariya ta kuma yi tunowa da maganar Asma’u da tace tayi hakuri wata rana sai labari, shi gani zai yi kamar an shiga rayuwarsa ne shida Fateema amma …