MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 30
MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 30 Hannu ya kai zai taba ta amma sai ya kasa, kallon bayan ta yake yi kawai zuciyarsa na tsananin harbawa.Tashi yayi ya koma gefen gadon ya dan zauna a hankali ya kira sunanta cikin sanyin murya a kuma dai-dai kunnanta yace. “Aisha bari muyi magana kota minti daya ce please.” Motsi INdo ba tayi ba bare yasa ran zata juyo ko ta tashi zaune, yana jin yadda take sauke ajiyar zuciyar ta amma ji yake tamkar tashi ake bubbugawa sabida tsananin yadda yakeji. Hannu ya kai ya riko kafadunta ta baya amma ko motsi bata yi ba ta dakire mai daga kwancen sai ya samu kanshi da kwanciya a bayan ta ya rungumeta a jikinsa tsam amma still bata motsa ba, ya dora kansa a wuyanta yana shafar kitson kanta zanan hannu, nan ma ko gezau lNdo bata yi ba. Duk wani hanyar lallashi da Sadeeq ya sani yabi lNdo dasu amma taki motsi duk da cewar tana numfashi hasalima idanunta biyu amma ya gagara ko mirgino da fuskarta gurinshi sabida yadda tayi mai taurin kai ta kafe a guri d’aya tamkar mutum m…