MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 28
MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 28 Tunda suka tafi koda wasa Sadeeq be taba gigin k’iran INdo a waya ba, bashi dama fa phone number dinta bare yace zai nemeta. A bangaranta itama bata ko tunaninsa tana gidanta hankalinta kwance babu abinda yake damunta. Ranar da su Sadeeq suka cika sati d‘aya da tafiya a ranar INdo ta fara fita, kullum tana gidan mak’ota bata nan layin bata can sam bata zama cikin kwanaki takwas mutanan unguwar sun santa maza da mata yara da manya. Yayin da a bangaran Sadeeq yana son ya kirata tunda yasan tana da hakki akan sa amma baya kaunar ya kirata tayi mai rashin kunya ko ta gaya mai maganar da zai kasa bacci dan ya lura akwaita da shuka magana ba kuma ta barinta indai harka gaya toh zata baka amsa hakan yasa ya shareta. Misalin k’arfe hud’u ta fito daga wanka tana shafa mai tajiyo me tallah a k’ofar gida, cikin sauri ta janyo doguwar riga a cikin wardrobe ta zura tare da d’aukar mayafi ta fita. A k’ofar gate d’in ta tsaya dan sake tabbatarwa da kunnuwanta abinda me talla…