MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 27

MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 27
MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 27 “Malam Sadeeq Kenan, ada kasanni ba yanzu ba.”  Shareta yayi ya nuna tamkar ma bejita ba ta juya tana kallonsa ta kuma daukar wayarta daya cillo mata. Madubin saitin kujerarta ta bude tana gyara fuskarta ya girgiza kai dan shi dama yasan da wahala yarinyar tayi hankali sabida babu arabi ba boko yaja tsaki har kusan sau uku sannan INdo ta kallesa tace.  “Babu kyau fa.” Yace “Ni zaki cewa babu kyau? Ko kin fini sanine da zaki cemin babu kyau?!”  “Allah ya baka hakuri, cewa akayi idan kaji wani ko wata sunyi abinda ba kyau ka tuna masa, toni tuna maka nayi.”  “Karki sake tuna min domin tun kafin kisan hakan nasani, ke karki sake yin magana har muje inda zan kaiki kina jina.?!”  Bata sake kula shiba har sukaje danja masu tallar abubuwa suka dinga dago musu taga me alawar madara da sauri ta zaro dari biyu ta mika masa ji Sadeeq kawai yayi tana cewa.  “Bani ta dika.”  Aikuwa ransa ya kuma mugun baci Allah-Allah yake kam a gama miko mata ya figi motar amma danja batazo kansu…