MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 26

MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 26
MUSAYAR ZUCIYA  CHAPTER 26 A bangaran su Sadeeq kuwa dakyar ya iya fita lecture, itama Fateema bata fasa yi mai breakfast ba sai dai duk babu wanda ya iya ci. Yana tafiya Fateema ta shiga cikin daki taci kuka sannan ta d’auki wayarta ta k’ira Ummanta, tana dagawa ta fashe da kuka hankalin Umma yayi matuk’ar tashi tana tambayar lafiya.  “Kiyi shiru kiyi min magana dan sai kin min bayani sannan zansan matsalarki.” Cewar Ummanta cikin lallabata dan ta gaya mata. Cikin kukan Fateema tace. “Umma Sadeeq ne ya kara aure jiya…”  Tayi maganar muryarta na hardewa hankalin Ummanta ya tashi tace. “Fateema a ina yayi auran bako labari?””Umma yazanyi matar d’an uwansa aka aura mai jiya shima be sani ba, sai da Abban su ya kirasa ya gaya mishi.” Ji tayi Umma ta sauke ajiyar Zuciya hankalin Fateema ya tashi tana cikin bargo amma wani irin mugun sanyi takeji yana ratsata,jita yi Umma na cewa. “0ho Allah sarki, Fateema toh karki damu kinga kema wannan kaddarar ba taki ta sauka a kanki ba, kiyi hakuri ki za…