MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 25

MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 25
MUSAYAR ZUCIYA  CHAPTER 25 Har sukaje gida Abba be sanar da Sadeeq ba, suna zuwa Abba ya shiga gida shi kuma Sadeeq daya kagu yaje gida ya juya kan motar ya tafi. Abba na zuwa fuskarsa cike da fara’a  ya cewa su Umma. “Toh hajiya Au an daura aure yau.” “Alhamdulillah Allah ya sanya musu albarka ya kauda fitina ya basu zaman lafiya.”  Cewar Umma nan da nan fa gida ya cika da murna lNdo kuwa bacci take a lokacin sai  bayan da ta farka ne Mama tace. “Aisha jeki wanka kizo kuje gyaran kai.”  Da sauri INdo ta mike cike da murna domin tunda ta dawo gidan bata sake koda lekawa kofar gida ba, sam sun hanata ko unguwa Mama zasu sai ta kafa mata doka akan idan ta kuskura ta leka waje, yau gashi zata fita kusan kwananta dari da takwas raban data kalli waje bare taga abinda yake wakana. Tayi kyau tayi haske fatar jikinta tayi luf-luf sannan tayi kiba da yake hankalinta a kwance yake suna kula da ita sosai dan ko ‘ya’yan gidan basu kaitajin dadi ba.  Wanka tayi tana fitowa taga saban dinki an dakko mata …