MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 24

MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 24
MUSAYAR ZUCIYA  CHAPTER 24 Koda sukaje kauyan Sani bakaramin mamaki Fateema tayi ba da ganin gidan su lNdo da kuma kauyan da suke, lallai Allah ya daukakata daya aura mata Abubakar har kuma tashiga wannan uban gidan wanda yafi nata komai da komai. Basu jima ba Sadeeq yace zasu koma ya bada dubu ashirin Inna da malam Hamza suka dinga yi mai godiya amma lNdo fateema kawai tayiwa sallama ta koma gida ‘yan garin suka cigaba da zuwar musu gaisuwa.  Rayuwa gaba daya ta sauyawa INdo komai yayi zafi tunda ta dawo kauyan Sani komai nata ya canza, tana takaba a gidan su kamar yadda malam Hamza ya bukata sai dai itace inzata bayan gida sai abata sanda da wuka wai ta tafi da ita ko idan zatayi bacci toh ruwanta a buta da wuka wai mijinta yana biye da ita duk da cewar ba’a gidansa takeba. Sannan ta dinga tafiya a hankali karya tadiyeta. wayyace haka ake zaman takaba?wannan ba musulinci ya koyar dashi ba kawai mutanene suka maidashi al’ada har hakan ya fara zama kamar ibada. Satin INdo biyu a gida lok…