MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 23

MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 23
MUSAYAR ZUCIYA  CHAPTER 23 Dakyar suka bareta daga jikinsa har rigarsa na yagewa da yake wani yadi ne ajikinsa 3 Quarter yayi saurin ficewa daga dakin lokacin gidan ya cika da mutane kasan cewar an kawo gawar. INdo kuwa sam bata yadda da cewar Abubakar ya mutu ba sai dai ta kasa dena kuka ganin yadda kowa yake kokarin ganar da ita. Da gudu ta shige toilet ta kulle kanta a ciki tana ta faman kuka da surutai barkatai, anyi-anyi ta bude taki kunsan cewar dama akwaita da taurin kai. Mintuna kalilan aka shirya Abubakar aka shigo aka sanar musu, Umma da Mama zasuje gurin gawar Abba yace su taho da Aisha. Kofar bandakin Umma ta tsaya tana kiranta  amma fur taki amsawa sai da Umman tace. “Aisha fito muje ki gansa da kanki.” Tanajin haka ta fito da sauri ko ganin gabanta batayi hijjab din jikinta yayi sharkaf da hawaye da majina suka riketa suka fita zuwa sitting room inda Abubakar yake a kwance a nannade, Sadeeq na ganinta yayi wuf yafice ga wani irin sarawa da kanshi keyi ko gani bayayi sai dai …