NAYI GUDUN GARA CHAPTER 17
NAYI GUDUN GARA CHAPTER 17 Zama tai ta bude flaks din, tiririn kazar ya daki hancinta, kallo d’aya tai ma kazarta san ba zata iya cinyewa ba. Tsam! ta mike ta kuma sauka kasan, dan dauko flate da serving spoon. Tana kitchen din ta ji dariyar laila sun fito falon. Flate din da cokalin ta dauko, da kunun aya a wani karamin jug, nan ta fito ta ajje kayan a kasa, ta jawo kitchen din, dan indai tana sama to kitchen din na rufe,kai tsaye ta wuce, sai kuma ta tsaya, saboda tunowar cewa sallama na daga cikin cikon addini. Sai alokacin tajuya idonta ya sauka akansu, sam basu lura da ita ba saida tayi gyara murya, ramadan ya waiwayo da sauri, sai ta yi dan yake tace “sannunku Amarya ya bakunta? Barka da rana my oga.” “Barka dai baby?.” Kallon da take mai, duk sai yaji kunya ta kama shi.Dan ya san kallon tuhuma ne, ganin ya shareta kwana biyu. A hankali ya mike laila dake gefensa ta hade rai tamau Kamar an aiko mata da sakon mutuwa. “Ya kadaici lad’ifa?.” Laila ta fada tana dan murmushin gulma. Sa…