NAYI GUDUN GARA CHAPTER 16
NAYI GUDUN GARA CHAPTER 16 Ladifa kuwa, mikewa tai zuciyarta na kuna! tai sama! Ji tai kishi na nanukar zuciyarta, tabbas! ta fara gane zama da kishiya a yau.Kuka ta sanya sosai Ta dade tana yi, sannan ta kunna Kira A wayarta, ta shiga bi sannu ahankali bacci ya dauketa. Wanda ko wanka bata samu tayi ba balleta canja kaya. Binta dakin yayi. Tana kwance tana danna waya. “Au! ba kiji bane.” Sai ta gyara zama ta juya. Hakan na nuni da ba zata tashi ba, dan ko motsi ba tai ba, sai ma rufe ido da tai. “Laila ba magana nake miki ba?.” “Ramadan dan girman Allah ka rabu dani na tsahirta.” Cafkota yayi ya murde bakinta, har sai da ta saki ‘yar kara . Kuma murde bakin yayi. Da karfi “Wato baki da kunya ko? Kin manta cewa I’m your boss KO? To ki kiyayeni, dan zaki sha wahala awajena idan baki nutsu ba.” Ba damar magana, saboda ya rike bakin tamau sai harara da take sakar mai,tana kokarin kwace kanta. Girgiza kai ya yi yana girmama halayyar lailar, da sam bai ankara dasu ba sai yanzu, hannunsa ya …