MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 22
MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 22 Harkasa INdo ta tsugunna tana gaida shi idanta akan fuskarsa tace, “Abba ina wuni?” Ya zura wayar cikin aljihunsa yana kallonta ya amsa. “Lafiya lau Aisha tashi kishiga daga ciki.” “Toh adawo lafiya.” Tafada tana mikewa ta nufi cikin gidan, tana shiga sallama tayi tana kiran Haleema kamar yadda takeyi idan suka zo gurin da zasu hadu. Haleema dake zaune a falo tajiyo lNdo na nemanta da sauri ta mike ta shige dakin su dan bata son su hadu a cikin wannan yanayin. Mata tagani a zaune a falo wasu sunzo wasu kuma na shigowa Mama 3 gefe gurin kujera ta takure Umma kuma a bakin kofa INdo ta dinga binsu da kallo kafin ta karasa kusa da Fateeman Sadeeq ta zauna itama ta takure tana gaida su, suka amsa mata a sanyaye. Juyawa tayi tana lekan fuskar Fateema wadda take faman hawaye a dai-dai fuskar tata tace. “Kai amaryar malam menene kike kuka? Ko malam Sadeeq ne,dan nasan shi sarai tun a makarantar mu meh yayi miki..?!” Zame jikinta tayi daga na lNdo tajuya tana kallon Ma…