MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 21
MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 21 Ganin yaki denayi mata dariya yasa ta lalubo towel dinta ta daura ta kwanta tare da janyo bargo ta rufa sabida wani sanyi dataji yana shiga cikin jikinta. A hankali ya matsa kusa da ita tare da zura hannunsa ya rungumeta tana jinsa amm ta kasa yin koda kwakwaran motsi sabida jikinta duk ya Iafa a haka bacci ya dauketa shi kuwa kasa yi yayi se tashi ma yayi yaje yayi wanka sannan yayi sallah ya d’auki sallayar ya maida ita inda zai dinga kallon fuskarta. Yana jan carbi yana shafar gashinta tare da shafar fashin goshinta wanda yake dansiriri. Har aka kira asuba lNdo bata koyi juyi ba bare asaran zata tashi ya mike daga kan sallayar yashiga bathroom ya tarar mata ruwa sannan ya fito, a hankali cikin nutsuwa ya fara tashinta amma babu alamarzata motsa sai ya yaye mata bargon ya fara kokarin kwance mata towel tayi saurin tashi tana rarumarsa tana furta “barawo.ta dauka barawo ne sabida a tunaninta wannan uban gidan baza’a rasa barayin dazasu shigo yi musu sata ba. …