ABUNDA KE BOYE BOOK 1 CHAPTER 1 HAUSA NOVEL

Tun da ta ji kalaman Bappansu na karshe cikin lumshe ido da qarfi tasakar musu wani irin tsumammen kuka me daga hankali tareda kara cukuikuyo shararar
ABUNDA KE BOYE BOOK 1 CHAPTER 1 HAUSA NOVEL
1️⃣ Tun da ta ji kalaman Bappansu na karshe cikin lumshe ido da qarfi tasakar musu wani irin tsumammen kuka me daga hankali tareda kara cukuikuyo shararar doguwar red colour bridal veil dinta daya rufeta rass har izuwa kasa kaidaga ganin yanayin shigarta kasan ta sabuwar amaryace wanda baifi mintina kadan ne ya rage adaura mata aure ba.. A hankli jikinta yake rawa rawa koinanta yadau kyarma tsaban takaici da wata iriyar matsanancin ruɗani dake famar cinta acikin ranta wanda bazata iya fasalta yawarsa ba, wasu maqudan hawaye ne kawai suka shiga gangaro mata akan fuskarta yuuu wanda daga ganinsu kasan bata shirya musu ba. yanayinta mai cike da jin tsoro da kuma tsananin tashin hankali tadada sunkuyar dakai ayayinda take agurfane a tsakiyar babban falon nasu zagaye da dattaijai  mutane hudu, inda tsiraran hannayenta da kafafunwanta masu sulbi da haske da sukaji wani irin hadadden xane na jan kumshi suke dafe akasa daf da inda ruwan hawayen nata ke diddiga kamar an kunnashi. kuka kawai take r…