BUZU BOOK 1 HAUSA NOVEL

Labarin BUZU ƙirƙirarren labari ne, duk wani sashi na labarin na iya faruwa a gaske, idan ya yi kamanceceniya da rayuwar wani ko wata arashi ne.*
BUZU BOOK 1 HAUSA NOVEL
BUZU  *Labarin BUZU ƙirƙirarren labari ne, duk wani sashi na labarin na iya faruwa a gaske, idan ya yi kamanceceniya da rayuwar wani ko wata arashi ne.* ⚠️ Labarin mallakina ne, ban yarda wani ko wata, su yi amfani da shi ta kowace irin siga ba, sai da izina. AISHA ADAM  (Ayshercool) 08081012143 Arewabooks; Ayshercool7724 Watpad: ayshercool7724 Page 1 Dare malafar rana, kowa ya bika ya shirya maka. Danƙareriyar mota ce, ƙirar highlander baƙa, take ta kwarara gudu a saman kwalta, tamkar hanyar domin direban kawai aka yi ta. Gefe da gefen hanyat baki ɗaya babu komai, banda yashin sahara, sai busassun bishiyu jefi jefi. Kasancewar dare ne, wata ya kai kwana goma sha huɗu, ya haska ko ina, ga taurari sun yi wa sararin samaniyar ado. Titin ta tsakiyar sahara ya ratsa, wadda yashin saharar ya bayar da sassanyan yanayi. "Kilomètre nawa ce ta rage mana ne?" Direban ya waiwayo ya kalli mai maganar wandaa fuskarsa a rufe take cikin rawani ya ce "Bai fi 95 kilomètre ba" "Dans  quelques…