YAR DANDI CE COMPLETE BY SAADATU BINTU ABDULLAHI
YAR DANDI CE COMPLETE BY SAADATU BINTU ABDULLAHI✍🏽 Alhamdullillahi am back again. *Bismillahirrahamanirrahim* 🅿️1 *JANAN HOTEL KADUNA STATE* Babban Hotel ne wanda ya shahara, ya kai ya isa, ya kasaita, yana daya daga cikin hotels din da mafita yawan mutanenmu na nigeria suka san dashi, mutanen mu na kaduna kuwa ya zamar musu abin alfahari kasancewar duk fadin kaduna babu hotel din dake tashe a halin yanzu kamar shi, Hotel din yayi suna iya suna kasancewar shi din kayatacce ne ya hadu iya haduwa, kama daga bakin get har zuwa cikin harabar hotel din, wasu labaran ma se in ka shiga cikin dakunan hotel din, sannan akwai tsaro Ainun a hotel din. In takaice muku duk wanda ka gani a hotel din to tabbas yanada abin hannun sa ne domin hotel din na masu hannu da shuni ne. Direct dancing hall na nufa, inda naga haske fayau kamar rana dukda kuwa tsakiyar darene dan a kalla ana neman 12:10am ne, amma kai kace tsakiyar rana ce. Hall din nada matukar girma. kafin na kaiga karasowa cikin hall din karar w…