GIDAN ANTY BOOK 2 COMPLETE

GIDAN ANTY BOOK 2 COMPLETE
GIDAN ANTY BOOK 2 COMPLETE  UNITED KINGDOM OXFORD A guje wata matashiyar budurwa tashigo cikin wani babban falo me shegen kyau, tana faman ‘kwalla kiran “momy ,momy”, shiru ba a amsaba, wata ‘kofa ta nufa bayan ta ajje wata hand bag d’inta meshegen kyau,”Momy,Momy” ta ‘karan ta fad’a da ‘karfi, wata babbar matace da taji wanka material peach colour me  shegen kyau, kyakkyawar budurwar data ke faman ‘kwalla mata kira ta kallah, cikin hausarta da har yanxu bata gama zama a bakinta ba ta furta “ Mimi, Yaushe zakiyi hankaline , bana hanaki wannan guje guje ba?”, a shagwa’be wacce a kira da Mimi ta ‘karaso zata rungume ta , Momy tayi saurin ja baya “ wallahi Mimi ki fita a idona , kinsan halina sarai “, tsayawa Mimin tayi kamar zata sa kuka “ Haba Momy na, kwanana biyu ban ganki ba amma da Alama ke ko missing d’ina bakiyi ba ,” ta’be baki momyn tayi , “ Allah ya shiryamunke “ dariya mimin ta saki tana cewa “Amin” kafun ta ‘kara da “ Momy albishirinki”, murmushi momyn ta saki kafun ta ce mata …