GIDAN ANTY BOOK 1 COMPLETE
GIDAN ANTY BOOK 1 COMPLETE
TAHEE!!! TAHEE!!! “Naam oumma “ cewar wata yarinya wacce kallo daya zaka mata kasan bazata wuce 16 to 17 years ba, ta fito daga cikin wata kofa da kallo daya zaka mata kasan daga kitchen take, sabida flour da ya Dan bata mata jiki.” Har hanxu baki gama kwabin ba , kinsan abbanku ya kusan dawowa kuma kinsan inyazo ya taddaku haka ran mune zai baci duka ko!”kiyi hakuri oumma na kusa gamawa TAHEER nake jira ya taimakamun …”bata kammala magana ba sukaji anshigo falan ko sallama babu, Mai da hankalinsu sukayi kan kofa . Wata yarinyace itama da bazata wuce 15 to 16 ba a tsaye sai faman ya tsine take kamar wata babba, kura mata ido TAHEE tayi dan jiranjin mai zatace, dan tasan zuwan ameerah ba alkairi bane. Kamar kuwa ta shiga zuciyarta , “maryam dake da TAHEE wai Kuzo inji abba…, bata kammala maganar ta ba sabida saukar marukan da taji a waje maban banta. Kuka ta saki mai kara tana jiyowa. Karo taci da TAHEER da TAHEERA a tsaye sai faman huci suke saki, TAHEE…