RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 8 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 8 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 8 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  Ya ce, “Ke! Ba wani wayo da zaki yi min. Cire ki ajiye rigar daban sannan ki dauki wannan ki gwada, kuma saura kiftawar ido goma in ce uku.” Da sauri ta cire rigar sai ta juya baya ta kuma kulle idanunta, sannan tasa hannuwanta ta harde, ta rufe kirjin. Dariyar shi ta kasa rukuwa sakamakon sikyat din da ta sa a jikinta, ta kuma daure da dankwali a kugunta, alamun yayi mata yawa sosai. Yayi dariya har da hawaye, ita kuma tana ta dan kukanta jikinta kuma yana ta ɓari. Ya ce, “Salma wannan siket din fa da ki ka daure kugu da igiya? Cikin kukan ta ce, “Ya min yawa ne, kuma bani da wani.” Yanda tayi maganar ya sake ba shi dariya. A ranta kuwa cewa take, “Mugu kawai, dole ka min dariya. ” Ya ce, “To kwance wannan madaurin.” Ta ce, “In na kwance zai fadi fa Yaya.” Ya ce, “Kin juya baya kina min magana bana jin me ki ke fada. Bari in zo in juyo da ke.” Ta ce, “Yi hakuri Yaya, Allah zan juyo.” Ya ce, “To j…