RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 12 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 12 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 12 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Www.bankinhausanovels.com.ng Mun tsaya Haka ko ya shigo dubata a ranakun da ba ya dakinta gaisuwa ke hada su. To bai san irin tarbar da zata yi masa ba yau. Ya fito daure da Tawul ya ganta cikin kwalliya ta aje masa goran ruwa da kofi a gefen gado kamar yanda aka saba. Ya kalle ta cikin murmushi, a ransa ya ce, “Yau da akwai abin arziki.” Ta miko masa kayan baccinsa yasa, ya dube ta. “Turarenki yayi min kamshi sosai.” Ta fadada fara’arta. “Haba?” Ya ce, “Sosai ma, za ki sammin?” Ta ce, “A’a, za dai ka dinga shakar sa a jikina.” Yayi ‘yar dariya. “Hakan ma na gode.” Ta ce, “Muje ka ci abinci ko? Kus-kus ne nayi maka da fa-dukan shi, yayi dadi.” Ya ce, “Lallai kuwa kin ce yau in ci har in kasa tashi.” Suka yi dariya gaba daya. Bayan ya gama da abincin kuma ya jinjina mata. Nafisa ta sha mamaki a kwanciyarsu, yanda ya tara da ita sau biyu a daran. Sannan da safe da yake Lahadi ce yana makale da ita sai gurin tara sannan ya tashi ya yi w…