RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 11 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 11 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 11 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Www.bankinhausanovels.com.ng Mun tsaya yunwa ga fuskarki ma duk a kumbure sai ka ce kin ci kuka?” Nafisa tayi rau-rau tare da fadin “Hmm! Bari Anty Maimuna, wallahi ina cikin wani hali a gidannan. Sai da nayi ta yiwa Mama mita a kan wannan auren ta ce ba haka ba, gashi yanzun tun ba a je ko’ina ba bakin ciki zai kashe ni.” Anty Maimuna ta zaro ido, “Fada min abin da ke faruwa don Allah, ke da mijin ko ke da kishiyoyi?” Nafisa ta soma kuka, “In su ne akwai wadda zan daga ma kafa ne? shi ne da kansa. kullum in dai yana dakina to fa sai sanda yaga dama zai dawo, in yi kwalliya in ta jiransa a banza. Karfe shida fa yake dawowa, amma ni jiya sai sha dayan dare. Nayi magana ya shiga fada min maganganu, har da yin yaji yana kwana a falo. Kuma gashi babu sirri, da safe yaje ya barbada ma matansa komai.” Ran Anty Maimuna ya baci, ta ce “To mene ne na zuwa ya fada musu don yaja miki raini?” Nafisa ta ce, “Hmm! Ni yanzun ban san ma me zan yi ba …