ZAFIN RABO CHAPTER 8 BY SAKIEYY ZAFIN RABO CHAPTER 8 BY SAKIEYY Www.bankinhausanovels.com.ng Nurse ce a gefan ta da take faman shirin mai da mata da drip dinta, sakeena na zaune tayi wani shiru, ga sauran matan gidan da duk suna tsaye sun zuba mata ido tun bayan dawowar ta daga wurin kamal, komai haushi yake bata, wani irin tafasa ranta keyi, tasan tana needing k’arin ruwa dan ta sami k’arfin jikinta da kuwa tayi d’an k’aramin iskokai ta kori kowa a d’akin harta nurse d’in dan tana buk’atar space, maida idanunta kan hannunta tayi da yake d’auke da igiyar drip wanda aka gama saka mata, “Kiyi hakuri ki gama wannan ruwan dan ki k’ara samin lafiya kuma ki d’an daure ki saka wani abu a cikin ki” Nurse d’in ta gaya mata, tana gama maganar ta ta fara kwasar kayan ta tayi waje, sisi ma binta a baya ta yi, suna fita bayan sun kullo k’ofa kan tayi wani kwakwaran mosti taga ummeeta da sarah a kusa da ita, har sai da suka bata tsoro, “Wanne had’add’an gayan da ya tafi yanzu? dan Allah a ina kika sanshi?” Duk kansu suka fad’a a tare,…