ZAFIN RABO CHAPTER 10 BY SAKIEYY

ZAFIN RABO CHAPTER 10 BY SAKIEYY
ZAFIN RABO CHAPTER 10 BY SAKIEYY Www.bankinhausanovels.com.ng  Bata tashi daga barci ba sai 10, tana farkawa tayi hanyar bathroom d’inta ta tsara wankan ta sannan ta fito, tayi shiriya cikan wata doguwar riga navy blue and pink ta material ta saka mayafi sannan tayi duk wani abunda ya zaman mata aladarta ta fito daga d’akin, amma sai da ta tabbata bata ji d’uriyar kamal ba, kitchen ta fara zuwa dan samar wa cikinta abunda zata ci, d’aura ma kanta tea tayi sannan ta d’auki bread tayi sandwich, sai da abincin ta yayi taci sananan ta k’ara dawowa kitchen d’in ta shiga dube dube, store d’in mak’il yake da kayan abinci da drinks ba abunda babu, tana bud’e fridge shima a cik’e taga su fruits, da vegetables da snacks da wasu drinks d’in, tana bud’e freezer itama tagan ta cikin da nama, su kaza su kayan ciki da dai suaran su, duk basu fara k’ank’ara ba alamun ba’a dad’e da zuba su ba, fitowa tayi da kayan cikin da kaji guda biyu ta ajiye a gefa, sannan ta shiga gyara su, sai da ta gyara su tsab…