UMM ADIYYAH CHAPTER 83 BY AZIZA IDRIS GOMBE UMM ADIYYAH CHAPTER 83 BY AZIZA IDRIS GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng lattin ofis.” Harararta ya yi, “Yaya Za ayi ki ce na je ofis yau?” Hannunta ya riko ya zaunar da ita a gefensa hade da tashi ya jinginu a jikin allon gadon. “Yau ne ranar da zan fara zama da ke, lokacinki ne, ba zan raba shi da kowa ba kuma. Don haka ki zo ke maa ki yi zamanki, ko kuma bari na shirya, sai na fito. Amma ba zuwa wurin aiki ba dai yau ba kam. Haba ai aka ganni a gun aiki yau, sai ace ba ki yi sa’ar miji ba.” Umm Adiyya tana dariya ta ce. “Kowa ya gani ya sani ai ba na kuma bukatar mutane su jaddada min komai.” “Aha, na san dai ba haka kawai na zama ad- dicted to you ba.” Ya fada yana shinshinan wani sabon kamshin da ya jiyo a bayan kunnenta. “Ka bari,” “Wannan meye sunansa?” Lumshe idanu ta yi, “Nafhatul ad-deeb.” “Hmm! Ina sonshi.” “Da gaske za ka sa na makara abin karyawa, yanzu yaran nan idan suka tashi ba su samu abinci ba, daga ni har kai sai mun rasa yadda za mu yi. Ga shi za mu wuce asibiti.” “Ni ban taba ganin rashin g…