UMM ADIYYAH CHAPTER 82 BY AZIZA IDRIS GOMBE UMM ADIYYAH CHAPTER 82 BY AZIZA IDRIS GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng iya numfashi, bare magana. Wannan shi ne babbar magana, wai dan sanda ya ga gawar SOja. A hankali ta juyo tana fuskantarsa, shi kuwa ya hada kansa da nata, idanunsa a lumshe, “Za ka ci abincin ko ka koshi?” “Zan ci, amma kar ki matsa.” Yau tata ta sameta. “Noorie..” Ta fada a sanyaye, gaba daya jik- inta ya mutu, “To yi hakuri, ka zauna sai na gama da wuri na zo, ka ji?” Www.bankinhausanovels.com.ng “Kin ga alamar zan ji rarrashinki yanzu?” Ya tambaya cikin wata raunanniyar murya. Ba ta ga alama ba kam, hakan ya sa ta kunna soket din ruwan zafin da ke gefensu kawai ta ajiye masu kwanon kayan fulawa, dangin su cake da dublan a gabansu Kujerar kicin din ya zauna ya ja ta jikinsa, suna cin kayan fulawan, suna shan shayin, koda yake shi ke ba ta Tea din a baki. “Uhm! Idan na yi motsi za ka iya kona mu.” “Idan za ki yi motsi, sai ki yi magana, na ajiye.” “Da gaske ka ke jin yunwa.” Ta fada tamkar sai yanzu ta fahimci me ya fada mata tun dazu. …