RAWANIN TSIYA CHAPTER 2 BY FADEELAH RAWANIN TSIYA CHAPTER 2 BY FADEELAH Www.bankinhausanovels.com.ng ALIYU BUGAJE (PAAPA)??+ Alhaji Muhammad Bugaje ya kasance mutumin qaramar hukumar Bugaje ne a cikin garin Katsina. Da shi da mai dakin shi Hajiya Aminatu sun haifi yaro daya kacal, Aliyu. Aliyu ya taso cikin gata domin kuwa mahaifin shi yana da arziki.. Sana’a ita ta kai mahaifin shi garin Kano wanda a nan garin Kano aka haife shi. Alhaji Muhammad ya kasance yana da kamfani na siyar da Rodi.. a wannan lokacin duk fadin arewa babu kamfanin da suke sayar da rodi mai kyau kamar nashi.. Yayi fice sossai a wannan sana’ar domin kuwa daga qasashen turai yake shigowa da su don haka akwai guarantee na lallai kayan shi masu quality ne. Aliyu dai tunda ya taso yake son harkar business kamar yadda ya ga mahaifin shi yana yi.. don haka ne ko da ya kammala secondary school dinshi a nan cikin garin Kano sai kawai mahaifin shi ya tura shi qasar America inda ya karanci Business administration a Stanford University. Aliyu dai bai bar qasar Ame…