RANA DAYA CHAPTER 9 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI RANA DAYA CHAPTER 9 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Www.bankinhausanovels.com.ng Mun tsaya suka amsa ya yi addu’a ga mamacin ya kuma ba Innar tasu magana sosai. Salma ta ce, “Inna wannan shi ne Alhajin nan da ya taimake mu.” Nan suka yi godiya. Ya mike ya fito tære da ce ma Salma “Zo mu je.” Ta taho haka. Yace “Ki saka hijabinki.” Duk da tsufan da kayan jikinta ke da su, da mataccen hijabin da ke jikinta bai ji kyamar bude mata gidan gaba ya ce ta shiga ba. Ita ma bata ji tsoron shiga ba, don sai take kallon shi kamar wani daga danginsu. Ya harba motar kan titi, sannan ya dube ta. “Kayan abinci zamu siyo, nasan su aka fi bukata yanzun ko?” Ta dube shi idanunta suka kawo ruwa. Ya ce “A’a kar ki min haka. Ba na ce ki daina kuka ba?” Ta runtse ido sannan ta sauke ajiyar zuciya. Ya kai hannu gefenshi ya dauko ruwan gora ya mika mata, “Amsa ki sha.” Ta amsa ta bude murfin roba ruwan ta daga tana sha, bata san tana jin kishi ba sai lokacin. Tas! Ta shanye ta sauke goran tana rufe murfin…