RANA DAYA CHAPTER 4 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI RANA DAYA CHAPTER 4 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Www.bankinhausanovels.com.ng Mun tsaya wannan mashirmancin ya zo da zancen zai auri mata uku rana daya, wannan ai labari yake yi. Dubi masu mace daya ma yanda suke fama a wannan zamani, ni dai na ce masa a’a ya dai zabi daya, in ma karin ne sai ya bari ya ga kamun Www.bankinhausanovels.com.ng ludayin zaman, in yaso can gaba ya kara.” Kaka dai ba ta ce kala ba, har Hajiya Halima ta kai karshe. Kaka ta ce, “Zubo min abin da ki ka zo da shi in lasa ko nafi samun abin fadi.” Dariya suka yi su duka sannan ta ce, “Farfesun kajin zan zubo miki, ko na kafar Sa? Sannan akwai kus-kus, ga kuma faten acca.” Kaka ta ce, “To fa! Duk a cikina? To zubo min faten sai ki sa farfesun kafar Sa din a ciki.” zubo mata ta bata sannan ta kwala ma Badi’atu kira, suka fito. Ta ce, “Ku je ku kawo ma Hajiya ruwa, sannan ku zo ku kwashe kulolin nan zuwa kicin.” Suka ce, “To.” Sai da Kaka tayi nak! Ta koshi, sannan ta kalli Hajiya Halima. “Zancen Shatima, ina son ki cire rash…