ZURI'A DAYA BOOK 4 CHAPTER 6 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI'A DAYA BOOK 4 CHAPTER 6 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 6 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  sun kara shakuwa sosai, domin ta gama gane Haaya mutuniyar kirki ce har ta ji tana daina kishinta saboda kyawun halinta ta ji tana jin za ta iya taimaka mata ta so Ya Abbanta, ba don wai ba ta son shi ba sai ganin kamar za ta iya ba shi farin ciki saboda ta karanci kyawun tarbiyyarta kamar ba wacce ta yi girman Turai ba, ko kadan cikin halayenta ba ta ga mara kyau ba, donhaka take jin idan Allah ya yi auran za su iya zaman lafiya, haka ta dinga jin kamar za ta iya bar mata shi. Da wannan ne ma ta fara jin gwara ta tsaya su kawar da matsalarsu ita da Mr. Sameer duba da zuciyarta ta kara jin za ta iya bar wa Haaya Ya Abba saboda son da take mata da kuma shakuwar da suka yi. Karfe biyar jirginsa ya yi landing Fu’ad da Al’amin da Kabir su ne suka je dauko shi a airport. Ya ji dadin ganin ‘yan uwansa haka suka taho suna hira har suka zo gida, nan fa ‘yan uwansa suka fito yara da manya kowa sai wani nuna farin cikinsa y…