ZUMA CHAPTER 9 BY SHATUUU ZUMA CHAPTER 9 BY SHATUUU Www.bankinhausanovels.com.ng Gabana nata faduwa na fita zuwa inda nasan tabbas zan same shi, inda kamar ance dole dole wajen zamu dinga zama muyi hira. Saboda gurin akwai haske saboda security light din yasa tun daga nesa na hango shi ya tsareni da idanu yana kallona, se naji yau idanun nashi sunfi kaifi akan ko yaushe, sunkuyar da kaina nayi ina wasa da yatsuna a haka ina tafe har na karasa. For some unknown reason se naji mun zama tamkar wasu strangers, kamar ranar ne haduwar mu ta farko dashi, na tsaya naki zama kuma na kasa daga idanuna na kalle shi balle nayi magana. Ajiyar zuciya ya sauke yace+ “Sahiba kinyi shiru, it’s been long ma da naji muryar ki. Talk to me!” A hankali se naji hawaye sun fara gangaro min kan kuncina, se naji maganar tashi tayi min fami, ban sani ba ko a cikin ku akwai wanda ya taba jin ciwo gurin ya fara warkewa kuma kawai se aka daye fatar aka kara maida gurin sabo, to wannan zafin haka na jishi cikin zuciyata. Bai lura da hawayen da…