ZAFIN RABO CHAPTER 5 BY SAKIEYY ZAFIN RABO CHAPTER 5 BY SAKIEYY Duk jikinta ba ya mata wani dad’i tun jiya bayan ta gane wa zata aura, jinta take yi daban, ba abunda bata sak’awa a ranta yanzu da take zaman jiran daddy ya dawo daga tafiyar da yayi, zuciyar ta ba abunda bata ce mata ba, har guduwa tace tayi amma ina baza ta iya ba, tana da hanyar da zata iya komawa wurin dangin mamanta amma in har ta gudu tabar gidan ba tama daddy adalci ba a ganinta, “Ke adalci yayi miki da zai miki auran dole” Wani b’ari na zuciyar ta ta fad’i, Sakeena saurin girgiza kanta tayi tare da kawar da tunanin da sauri, tana cikin wannan taji an tab’a ta, tana maida idanunta wurin taga wata k’anwar mommy ce me suna Maryam a tsaye, Maryam d’in ta girmeta amma ba sosai ba, kuma ba laifi suna shiri, tama fi shiri da ita akan shaheeda, duk da akwai aminci tsakanin su bata ji dad’in ganinta a wurin ba, dan tana so ta kad’ai ce ita d’aya dan hayaniya bak’i ce da suka cika gidan ya dameta shi ya saka ta fito garden d’in gidan dan Shan iska da samu t…