ZAFIN RABO CHAPTER 3 BY SAKIEYY ZAFIN RABO CHAPTER 3 BY SAKIEYY Www.bankinhausanovels.com.ng Sakeena na ajiye faiza da faheema a hotel d’insu tayi hanyar gida bayan sunyi sallama sosai, tana isa tayi parking ta fito, ta fara takawa zata shiga cikin gidan tayi kicibis da daddy, yana zaune a compound d’in da newspaper a hannunshi alamun karantawa yake, ji tayi gabanta ya fad’i dan bata gaya mishi zata fita ba mommy ta gaya ma, ta sauri tayi ta k’arasa inda yake ta tsgunna har k’asa ta fara mishi barka da rana, jin muryar tan da yayi ne ya dakatar dashi daga karatun jaridar da yake, gyara reading glasses dinshi yayi sannan ya mai da idanunshi kan Sakeena wace ta sunkuyar da kanta tana kallon k’asa, tambaya ya shiga yi mata daga ina take, gabanta ne ya k’ara mummunar fad’uwa ta tabbata in har yasan daga wurin su faiza take sai ranta yayi mugun b’aci, tunda kanta na k’asa bazai gane bata da gaskiya ba ta shirya mishi k’arya cewa wani aiki taje ta k’arasa a office director d’in yace lallai da gama kan gobe wato ran littini…