TSINTACCIYA CHAPTER 6 BY NIMCY LUV
TSINTACCIYA CHAPTER 6 BY NIMCY LUV
Kuka Meema ta sanya wanda ya Ζara tayar da hankalin President Ahmad Adil,cikin damuwa yace “he looses his memory? I understand,but problem Ιin fuskar fa? How long zai kasance cikin rashin sanin wane ne shi?” Kafin Dr yay magana Meema tace “i don’t understand Dad,loosing memory kamar ya?” Cikin nutsuwa Dr Ιin ya kalleta kafin yace “everyone forgets things atimes,how often have you misplaced your car keys or forgotten the name of a person you just met,some degree of memory problems as well as a modest decline in other thinking skills,is a fairly common part of ageing,there’s a difference,however between nrml changes in memory and memory loss associated with alzheimer’s disease and related disorders,and some memory problems are result of treatable condition Madam Meema Ahmed Adil” shiru tayi idanunta yay rau rau zai kawo ruwa kafin a hankali tace “kenan bazai iya tuna waye shi ba? Balle ya tuna abinda ya faru dashi,more explanation please” farin glass Ιinsa ya Ιauka tare da sanyawa cikin nutsuwa yace da Meema “he looses his memory,he can’t remember anything about his life,and normal age-related kin gane ba? Memory loose doesn’t prevent you from living a full productive life for example,you might occasionally forget a person’s name,but recall it later in the day,amma tunawa lokaci guda it’s difficult,you might misplace your glasses sometimes,or maybe you need to make lists more often than in the past to remember appointment or tasks. These changes in memory are generally manageable and don’t disrupt your ability to work,live independently or maintain a social life” Dr ya Ζare maganar yana sauke numfashi baya jin hausa ko kaΙan hakan yasa dukkan wani bayani da zai yi dole sai dai yay da yaran nasara Ingilishi kenan.
Kasa magana Meema tayi bata san mene yasa ba amma wani mugun jin tausayin mutumin take kafin a hankali tace “alright yanzu dole sai the same abinda ya faru da shi ya sake faruwa zai iya tuna waye shi?” Ta faΙa abinda Dr Ιin ya faΙa,jinjina kai yay kafin yace “sure” miΖewa President Ahmad Adil yay yana kama hannun Meema kafin yace “Dr ka shirya komai na tafiyar cikin week Ιin nan za’a fita dashi” ya faΙa yana jan Meema zuwa waje,kallonsa tayi tana kwaΙe fuska kafin tace “Dad” ba tare da ya kalleta ba yace “what again Meema?” Idanunta na kawo ruwa tace “Dad i want see him please! Please Dad” tsayawa yay yana kallonta kafin yace “Look Meema wannan ba age Ιin soyayya dashi bane,infact kin girme masa respect yourself ok?” Ζasa tayi da idanunta tana jin ranta babu daΙi kafin tace “Dad ni fa ba?” Tsareta yay da idanu kafin yace “kefa mene? Uhm gayan naji” girgiza masa kai tayi kafin tace “nothing” kama hannunta yay tare da shiga cikin mota securities suka rufa masu baya.
Can cikin gidansa suka nufa bayan sun Ζarasa Meema ta fito da sauri ba tare data tsaya Dad Ιinta ba,murmushi kawai Dad yay domin hakan da tayi yasan fushi tayi.
A bakin shiga lift ya sameta tana ganinsa tai saurin shigewa tana danna 3rd floor,rabuwa yay da ita ya nufi wata daban yana shiga ya danna shima,a parlor ya sameta tana maΖale jikin Mom tana surutai wanda ita kaΙai ta san mene take cewa,kallon juna sukai shi da matarsa kafin Mom tace “yanzu kuka fita lafiya amma ji har abin ya motsa” cike da so da Ζaunar Ζ΄ar tashi ya kalli Meema wacce zufa ke yanko mata sai surutu take ita Ιaya murmushi yay kafin ya Ζarasa tare da kama hannunta yace “Allah sarki Mamana,Ubangiji yana sane dake kinji nothing will happened to you again,ina nan kinji i’m always be by your side kinji” ya faΙa yana yin gaba da ita tare da nufar side Ιinta,suna zuwa ya zaunar da ita bakin bed kafin ya fara bin bedroom Ιin da kallo,a hankali ya Ιauki wayarta tare da kunnawa yace “ke Ζ΄ar gidan shugaba ce,President’s daughter,ya kike son maida kanki middle class ne eh? U have to be classes lady irin manyan matan nan,ni da na keso ki fara fita kina rage min wasu manyan ayyukan tunda kinga ba ni da wanda zai taimake ni ba ni da wani babban Ιa,soon zaki fara fita zuwa wasu Company,wai ke nan sunan babbar likita,a haka zaki zama babbar baΖuwa a wajan taron sickler day Ιin,haaaa! TaΙ su Meema Ζ΄an Ζasa na gari a nan tare dasu I.d card voters card anya kin taΙa voted na Dad Ιinki ma?” Murmushi tayi masa tana Ζwace jakarta bai kulata ba,a hankali ya zauna a gefe ganin wayar nata empty ba komai gata sabuwa dal iphone 13pro max,transfer kati yay mata na 50k kana ya sai mata data cikin sauri ya shiga play store tare dayi mata download na I.G whatsapp,twitter sai wattpad da okoda books tare da games da app na qur’an da azkar,buΙe mata komai yay da wani special name Meema_ President’s daughter,wayarsa ya Ιauka tare da yi mata sending na picture Ιinta,Ιora mata shi yay saman profile kana ya bata yana faΙin “yanzu kika fito Mamana,oyah tashi ki fara duba wayanki gashi nan ki yi abinda kike so na tura maki 500k a acct naki” dariya ta masa tace “thank you Dad i love you” Murmushi yay mata yana miΖewa yace “love you too Meema,kinfa girma good 32 to 33 yrs amma abu ya saki gaba kamar yaΖi please ki yita addu’a,ki samu kiyi aure kamar ko wacce mace i don’t know what wrong with your mother bata damu ba sam,ina cikin mutane hankalina na kanki ki taya ni kula da kanki,ahha! Ba na son facebook domin zaki iya gani ana zagin Dad Ιinki ranki ya Ιaci,ina yin abinda naga zan iya,amma kin san halin mulki,mai makon jama’a su tayamu da addu’a sai su bimu da zagi,bayan bama da laifi domin na saman su ke take komai,ki kula da kanki akwai guards naki guda ashirin duk inda zaki,make sure tare kuke,ok?” Jin shiru yasa ya juya,ashe tuni bacci ya Ιauke ta shi kaΙai yake abinsa,girgiza kai yay tare da Ζarasawa wajanta ya gyara mata kwanciya,a hankali ya shafa kanta tare da sumbatar goshinta,fita yay yana rufe mata Ζofar bedroom Ιin.
Washe gari Dad da wuri ya fita zuwa wajan meeting wanda zai zauna da Ζ΄an majalisu na dokoki wato _(National assembly)_ na Ζasa baki Ιaya,akan lafiya musamman ciwon sikila wanda ya zama kamar Annoba.
A hankali Meema ta fito sanye da silhouette da VGOLD palazzo trousers wanda yake da faΙi sosai daga Ζasa kamar skirt daga waist Ιinta kuma ya Ιame ta irin sosai Ιin nan ba zaka taΙa cewa tayi shekaru har 33 ba,tayi rolling kanta da wani haΙaΙΙan vail,a hankali take tafiya kamar wata Ιarauniya tazo dai-dai parlor taji ance “mrng mai satar hanya” ajiyar zuciya ta sauke tare da faΙin “Mom” sai kuma ta juya tana murmushi,zama tayi tace “mrng Mom?” “Mrng how are you? Ina zaki haka ko breakfast baki ba?” Shiru tayi sai kuma tace “kamar nayi ko? A’a banyi ba,kai na yi” girgiza kai Mom tayi tana ajiye system Ιin gabanta,wato al’amarin Meema kullum Ιaci yake kamar da sauΖi sai kuma ta Ζara komawa ruwa “bama ki tabbar kinyi ba kenan ko,eh?” TaΙe baki tayi domin Mom faΙa gareta yanzu zata hargitsa ta,miΖewa tayi ta fice daga cikin gidan baki Ιaya.
A can waje kuwa wata mota ta shiga cikin sauri guards suka nufota,da sauri ta Ιaga masu hannu driver yaja da gudu tana faΙin “aso rock clinic gulps za kai dropping nawa” ta faΙi hakan tana buΙe network Ιin wayarta,kai tsaye wattpad ta shiga ta fara dube dube domin tun sanda Dad yay mata settings Ιin komai bata taΙa wayar ba sai yanzu,har ta shige wani book sai kuma ta dawo baya taga ansa _Our secret_ (Sirrin mu) shiga tayi tana zaune ta karanta Episode 1 to 5 lokacin da tazo wajan da Airah ta kewa Sheikh kiss kanta yay wani mahaukacin sarawa a firgice kuma tai wani irin….
Dafe kanta Jikinta ya shiga mahaukacin rawa jijiyoyin kanta suka mimmiΖewa, wasu abubuwa suka fara gilmawa ta cikin idanunta a hankali kuma take lumshe idanunta cikin nutsuwa bakinta yake motsawa a hankali take furta _“Ya hayyu ya Ζayyumu”_ shine kawai abinda yake faΙa drivern ne ya Ιan tsaya da gudun da yake tare da juyawa ya kalli Meema cikin girmamawa da bata matsayinta yace “Madam is everything okay?” Jinjina masa kai kawai tayi a hankali tai baya tana kwanciya a jikin kujerar motar da sauri kuma ta Ιauki wayar ta tura ta cikin hand bag Ιinta.
Ganin sauyin yanayinta yasa Driven ya fara da ita a hankali har suka isa clinic Ιin fitowa yay da gansa sosai mamaki ya kamasa ganin bacci take hankalinta kwance babu abinda ya dame ta, ya daΙe tsaye a kanta yama rasa mene zai mata, a hankali ya fara buga kujerar da take kai yana faΙin “Madam! Madam!” Idanunta ta buΙe tana ya motsa fuskarta ba tare data kallesa ba ta fito daga cikin motar kai tsaye cikin haΙaΙΙan Clinic Ιin Wanda Manyan likitoci suke ciki tana shiga Dr dake kula da mutumin ya fito Murmushi Yay mata yace “wlcm Madam Meema Ahmed Adil” Murmushi tayi masa wanda ya sanya yay Ζasa da kansa domin kwarjini gareta sosai ga shirme da manta abubuwa gaba Ιaya kanta bashi da saiti “how can i help you?” Taji Dr Ιin ya faΙa cikin Ζasa da murya tace “please ina son nai magana dakai prvtly firstly kuma ina son ganin sa please kaji?” Jinjina mata kai yay kafin yace “follow me” bayansa tabi tana sakin murmushi a cikin wani haΙaΙΙan room mai masifar kyau ba zaka taΙa cewa mara lafiya bane a ciki waje ya bata ta shige ciki idanunta na kansa, yana kwance flat gaba Ιaya an sanya masa wasu na’ura a jikinsa fuskar nan nashi manne da bandeji kansa ma haka, baΖi ne his Elegant black skin Ιin nan nashi sai Ζyalli yake, babu abu mai haske a Jikinsa irin foot Ιin sa da tafin hannunsa a hankali kuma Numfashinsa ke sauka, he’s dark-skinned yet handsome zai iya shekaru 29 to 30 kujera taja ta zauna kusa dashi a hankali ta kama hannunsa idanunta na kawo ruwa cikin Ζasa da Murya tace “you’re my brother as frm today, I’ll take good care of you kaji babu abinda zai sameka, i love You irin so na Ζ΄an uwa in sha Allah zaka tashi you’ll be fine ji nake kamar na sanka tun can baya” Shiru tayi kafin ta Ζara riΖe hannunsa tace “Nima zaka zaka kula dani ko? I’m scared ina jin tsoran mutane, kaga nan nima wai babba ce fa kullum Dad sai yace na zama babba classes lady zaka kuya min komai ai ko? Zaka dinga zuwa mall mall dani da park za muna hira ko?” Ta faΙa hawaye na sakko mata, mamaki ne ya kama Dr domin yaji ana faΙin Meema bata da wani cikakken hankali shiyasa mahaifin nata baya fita da ita amma the she’s talking yanzu zaka Ιauka mai cikakken hankali ce Allah Al-hakkamu kenan.
Murmushi ta saki jin ya riΖe hannunta dake cikin nasa, juyawa tayi ta kalli Dr hawaye da dariya na kwance mata tace “You see ba? I’m lucky wallahi he loves me I’m so happy” ta faΙa kuka na Ζwance mata kamar wacce ta tuna wani abu kuma ta miΖe tsaye tana kallon Dr kafin tace “let’s go” fita yay tana biye dashi a baya har office Ιinsa zama yay kana ta zauna tana faΙin “i need your help Dr but kada Dad yaji please” jinjina mata yay kafin yace “what the you want?” Shiru tayi tana tunani sai kuma tace “Ina son a sawa wannan mara lafiyar fuskar wani” idanunsa ya ware yace “fuskar wa kikeso asa masa to?” Ya faΙa cikin harshen turanci “bani da photon sa amma dai ina da photon a idanuna da zuciyata” Wayarsa ya Ιauka yace “ok bari na kira arteries muga” tana zaune yay waya not too long wani mutum ya shigo Ιauke da kayan drawing ajjiye komai yay a hankali Meema take masa bayanin komai tana faΙa yana zanawa Murmushi tayi tana jin wani mugun daΙi na ratsa Zuciyarta ta sauri Dr ya miΖe tsaye idanunsa akan zanan cikin Ιaga murya yace “wannan ai photon tsuhun Ιan majalisa ne (Members federal house of Representatives) Hon Bukar Bello..
A hankali yake sakkowa daga strains Ιin benen yana sanye da wata Ιanyar shadda fara dal da ita Ιinkin babbar riga da jamper, ya Ιura wata half jaddara a saman sumar kansa wacce tayi kwance lubb da ita, Ζafarsa sanye cikin wani Black half shoe na Gucci mai tsananin kyau.
Yana tafe yana maΖala Rolex Ιinsa na A.lange & SΓ²hne yay wani irin mahaukacin kyau idan kaga Akeem zaka Ιauka wani Balarabe ne fuskarsa tai wani fresh ga wata haiba da zallar nutsuwa fuskar nan babu yabo babu fallasa as usual yana tafe yana lumshe idanunsa tare da motsa bakinsa.
Abbu dake downstairs yace “Akeem yau dai ka makara kamar ka manta yau Friday” caraf Didi ta amshe zan can tana faΙin “yoooo Allah na tuba zuciya ce babu alkairi, mugun abu yay masa yawa faΙa yake nema dani saboda an faΙa masa ni sallamammiya ce irinsa to ba’a gantale nake ba, wallahi Bukari ina faΙa maka kaji tsoran ka nemawa Ιan ka magani gani kuke ina wasa amma billahi wannan yaron ba lafiya ce dashi ba” Murmushi Abbu yay yace “Didi kunfi kusa da mijin naki fa” wani zaro ido tayi tace “wa Ιin? To wallahi li’ilafi Ζurash banda a ido aka haifi Audil wallahi da cewa zanyi ba jinin ka bane, saboda tsabar maita ka kalli yadda yake jajir dashi kamar wannan yaron na yama sunan Film Ιin…” Ta faΙa tana kallon Afaf wacce ta fito daga part Ιinsu da sauri Afaf tace “Shuria khana, na Film Ιin maheyk” tafa hannu Didi tayi tace “Yawwa Shimam irin albarka shifa kai Muhammadur Rasulullah s.a.w wlh mugun halinsu Ιaya” A hankali Akeem ya gama sakkowa tsittt wajan ya Ιauka sai muryar Didi ta fara faΙin “Astagafirullah satali saboda Annabi albarkacin juma’a” Murmushi kawai Abbu yay a hankali yay gaba Akeem ya fara masa baya kamar wasu abokai kai tsaye mota suka nufa gaba Ιaya kuma back seat suka shiga driver yaja sun Ιan fara tafiya Abbu ya kalli Akeem yace “Ina son sanya Akeela makaranta what’s your opinion?” TaΙe baki yay ba tare da yace komai ba ganin hakan yasa Abbu faΙin “Abdul-hakeem” marai-raice fuska yay kamar zai kuka yace “for God sake Abbu mene nawa ni” da mamaki Abbu yace “Akeem! what wrong with you? Ζ³ar uwar taka jikinka itace Meye ruwanka cikin lamuranta Are You at of your sense?” HaΙe fuska Akeem yay ba tare da yace komai ba a yanzu haushin yadda Abbu yake son fifita shi da village gal Ιin nan ya keji cikin damuwa Abbu yace “ashe zaka iya wulaΖanta jinin Ιan uwana jinin Baffanka har haka Abdul-hakeem? Akeela is your sister kamar Aleema da Afaf mene yasa kake haka ne?” Ζata rai yay yana sauke numfashi kafin yace “Abbu ni kawai i hate her ne” wani sassanyan numfashi Abbu ya sauke yana mai jin daΙin hakan a ransa shi kaΙai yasan mene zuciyarsa ke faΙa masa a haka suka Ζarasa babban masallacin juma’a dake nan nasarawa gra.
A can gida kuwa su Akeem na fita Akeela ta fito a sanyaye kamar wata munafuka tana sanye da wata haΙaΙΙiyar open abaya blue black ta Ιura wata hula mai gashi a kanta, cikin nutsuwa ta Ζarasa shigowa ciki ganinta yasa Ummi faΙin “Daughter kin fito?” Ζasa tayi da kanta tana wasa da yatsun hannunta MiΖewa Mami tayi tare da barin main Parlo Ιin gaba Ιaya taΙe baki Didi tayi tace “to ita dai rayuwar guda nawa take? Ban dai gantalewa da son zuciya irin na mutum, idan ka riΖe Ιan wani baka san wazai kula da naka ba fisabilillahi mugun abu Ζarara” Murmushi Ummi tayi tace “have a sit daughter” Afaf ce ta kama hannunta tana faΙin “Ummi wallahi tsoran Hamma Akeem take kamar ranta” taΙe baki Aleema tayi tace “ba dole ba, mutum sai faΙa da miskilanci wallahi gabana har faΙuwa yake idan na jisa kai wallahi munyi missed Hamma Adnan Allah ya dube mu” Ummi dake MiΖewa domin haΙa lunch tace “Za kuyi bayani bari yazo” da sauri Didi tace “Tsila (Akeela) ke dai babu ruwanki da shiga tsabgar wannan mutumin kada kuma ki biyewa su Shimam wallahi shawara nake baki bani da mugun abu ko kaΙan” ita dai Akeela da idanu kawai take kallonsu kafin tai magana taji Ζamshin turarensa da kuma zazzaΖar muryarsa yay sallama cikin parlon Abbu na bayansa da sauri ta kulle idanunta Ζirjinta na wani irin bugawa, babu wanda ya kalla cikin parlon part Ιin Mami ya nufa tana zaune a Parlon ta watching TV Akeem yay sallama Murmushi tayi tace “wlcm Hero” shigowa yay tare da zama saman sofa yana Ιan lumshe idanunsa kafin a hankali yace ” Ma’ul khair Mami” Murmushi tayi tace “yawwa yaya aiki?” Yana lumshe idanunsa yace “Allahamdulillah Mami” kafin Mami tayi magana Amani ta shigo tare da faΙawa jikinsa tana faΙin “Abbie na” satar kallon Mami yay yaga basu take kallo ba da sauri ya rungume Amani yana bata peak a goshinta yace “little na” dariya tayi tace “Abbie na kayi kyau kamar new Aunty” ware idanunsa yay irin bai gane ba Ιin nan tace “Abbie Anuty Akeela tana da kyau” haΙe fuska yay yace “ΩΨ§Ψ£Ψ±ΩΨ―Ψ§ΩΨ΄ΩΨ΄Ψ±Ψ©” (ban son surutu). Shiru tayi masa domin tasan halin Abbien nata miΖewa yay Mami tace “Uba da Ζ΄ar duk babu kunya ka daure dai kayi wani Auran a samu more children’s” shafa fuskarsa yay tare da Ιaukan Amani ya fita, ita kaΙai ce a parlon duk sun tafi taya Ummi shirya Lunch can nesa da ita ya zauna domin yunwa ya keji shiyasa ba zai iya komawa part Ιinsa ba, buΙe ido tayi a hankali tare da sauke ganinta a kan Ζwantaccen sajansa wanda yay mata masifar kyau bata taΙa ganinsa da manyan kaya ba kenan sai Friday Friday yake sawa? Ta tambaya a ranta, wani irin sahihin kyau yay kamar Balarabe Amani dake jikinsa ta zame tace “Abbie ka ganta tana da dimples irin nawa da naka Allah” Murya can Ζasa dai-dai kunan Amani yace ،Ψ£ΩΨͺ” Ψ₯Ψ¬ΩΨ³ Ω ΨΉΨͺΨ²ΩΨ§” Wato _Ke! Zauna dai-dai_ jin abinda yace tayi shiru tare da komawa ta zauna tana jan gemunsa.
Fitowa Abbu daga part Ιinsa idanunsa akan Akeela ganin Akeem zaune a parlo abinda bai taΙa ba kenan yasa kawai ya nufi dinning room gently Akeem ya miΖe da sauri Amani ta zame hannunta ta nufi wajan Akeela ogan kuwa tunda ya zauna bai kalleta ba, tana jin Ummi na kiranta kasa tashi tayi domin jinta take wani uncontactable a cikin su.
Bayan sun kammala yin lunch Ιin Akeem ya haura sama Abbu kamar yay ihu ya keji domin tun safe bai samu damar yin magana da Akeela ba bare yaga Ζ΄ar shagwaΙar data saba yi masa.
Da daddare bayan sallar IsshΔ duk suna zaune a parlo iya yaran Aleema, Afaf da kuma Akeela Amani tuni tayi bacci ya jima da shigowa amma gaba Ιaya basu san ya shigo ba hankalinsu na kan film Ιin This is fate da ake na karan da firita, gyaran murya yay yana zuba hannayensa a cikin hannun jallabiyar jikinsa da sauri gaba Ιaya suka juya tare da kallonsa a kusan tare da Afaf da Aleema suka shiga faΙin “lailatan Sa ida” wato barka da dare haΙe fuska Akeem yay cikin wata tsawa yace “duk Shegiyar dana Ζara gani da Wannan kayan uhm” ya faΙa yana duban Ζananun kayan dake jikinsu bakin Aleema na rawa tace “Ayyah Hero banmu Ζara sawa” wata tsawa ya daka mata yace “ku Ιace min da gani” Akeela tafi kuwa firgita jikinta na wani irin Ιari ta miΖe zata gudu da wani irin sauri yasa hannunsa ya riΖe wist Ιinta tare da wani irin juyo da ita ya haΙata da…..
Post a Comment for "TSINTACCIYA CHAPTER 6 BY NIMCY LUV"