TSINTACCIYA CHAPTER 3 BY NIMCY LUV
Www.bankinhausanovels.com.ng Jiyayi Numfashinsa na wata iriyar fusga lokacin daya sauke idanunsa a saman Ζirjinta, cikin sauri ya zame idanunsa yana shafa fuskarsa.
Bai taΙa ganin halittar da yaji yana mutuwar so, irin son nan mai zautar da mutane irin Akeela, at least zai iya good 35yrs ko sama da haka, kusan jiΖarsa ma take ba Ζ΄ar ba, ko zai haΙata da yaransa sai dai suyi age mate da Aleema.
Malam ne yay gyaran murya kafin yace “zauna mana Bukar” zama yay still idanunsa akan fuskar Akeela kamar zai haΙiye ta, saboda wani mugun kyau da tayi masa a fuska, ga Ζirjin nan dam, so Ma sha Allah, But even her lips are looking luscious succulent and irresitable every tensed man.
Shafa fuska ya sake yi kafin yace.
“Baffa badai Akeela tayi wannan girman ba?” Murmushi Baffa yay yace “Wallahi Bukar” “Allah sarki, the last time dana ganta tana primary 2 ne” cewar Abbu ya faΙa murya a shaΖe.
A sanyaye Baffa yace.
“Kayi hqr Bukar garin ceto Ζ΄ar dana haifa Ιan cikin ka yay asara nasa rayuwar” kamar Baffa zai kuka saboda damuwa cikin damuwar shima Abbu yace “haba Baffa, da abinda ka haifa da nawa ai duk Ιaya ne ko? Blood is thinker than water, koni i can do anything for this innocent gril, she deserved it” Murmushi Baffa yay zuciyarsa na masa zafi sosai Kafin yace.
“Ban san mene yasa Akeela tayi hakan ba, tana da hankali amma lalurar da Ubangiji ya jarabce ta dashi na neman zautar da tunaninta” da Mamaki Abbu yace “lalura?” “Eh! Tana da Amosa nin jini (SIKILA), wanda ke sonta tunda yaji labarin ciwonta yace ya fasa, bazai iya zama da mai ciwon SIKILA ba, haka nan taje ta shafa masa, shiyasa na yanke shawarar bawa wani auranta mai suna Malam Buba, yana da mata uku yara goma tsoho ne domin ya girme min, yace yaji ya gani zai zauna da ita a hakan, tun lokacin Akeela ta daina walwala na san bata son shi, to idan bata Aure sa ba wane zata aura? Eh? Kasan yadda ciwon SIKILA yake kamar Annoba a wannan lokacin musamman a wannan lokacin damuna da muke ciki, wannan dalilin yasa ta nemi kashe kanta ta wuta da bala’i”
Shiru Abbu yay Mamaki duk ya kamasa, yarinya like Akeela da ciwon SIKILA? Allah Al-hakkamu kenan bowayi gagara Misali.
Gyara zama Abbu yay cikin serious tone voice yace.
“Cutar sikila ko amosanin jini na Ιaya daga cikin cututtukan da za’a iya cewa na neman zama ruwan dare, saboda yadda ake yawan samun yin aure tsakanin masu rukunin jini AS da AS ko SS da AS, amma Abu mafi muhimmanci Shine babu yadda za’ai ba tare da gamayyar Ζwayayen haihu ba mutum ya samu SIKILA, babban jahilci ne ma gamai cewa za’a shafa masa, ai ba tari bane, ko H.i.v SIKILA zan iya haΙata da Asthma, amma Baffa batun zaka aura wa Akeela wani can banza bai taso ba, kai mata aure inda ake sonta kuma za’a kula da ita, na tabbatar he loves her just of her beauty and..”
Shiru dan baya jin iya cewa wani abun.
A hankali Baffa yace “To Bukar yay zan? Wayewar inda kuke da nan akwai bambanci sosai” idanunsa akan Akeela yace “Allow me to go with her, ka bani ita, zan haΙa ta da miji na gari wanda zai kula da ita, tai cikakken ilimi inda zakai farin ciki zan haΙa ta da yarana” ya faΙi maganar ba tare daya shirya ba, domin ji yake ko mintina goma bazai iya ba tare daya kalli Akeela ba, yay hakan ne saboda ya samu very close to her ya dasa mata masifafan son sa a Zuciyarta wanda Turawa suke cewa _ETERNAL LOVE_ yasan kuma soyayyarsa da ita ba zata taΙa zama _FORBIDDEN LOVE_ ba.
Jin muryar Sarkin ruwa a bakin Ζofa na sallama yasa Baffa MiΖewa cikin sauri yay waje.
Yana fita Abbu ya miΖe, cikin tafiyar nan wacce ya kejin kansa ontop, a hankali ya Ζarasa inda Akeela ke shimfiΙe kamar ma matacciya,
Ζirjinta dake sama da Ζasa ya kalla ganin hakan yasa ya tabbatar she still alive.
Tsaye yay a kanta yana sauke numfashi tare da lumshe idanunsa slowly kuma ya Ζara buΙe idanunsa, kamar zai juya sai kuma ya sunkuya dai-dai kanta yana Kallon Zallar kyan fuskarta.
Hannunsa ya sanya ya Ιan Ζara zame zanin kanta nan take sumar kanta ta bayyana irin sosai Ιin nan gata rabi baΖa rabi jaa.
Wani cute smile yay yana yin Ζasa da bakinsa zuwa saman fuskarta bakinsa ya manna a goshinta tare da bata wani special kiss wanda ya kejinsa best kiss in his whole life.
Baffa ne ya kalli Sarkin Ruwan kafin yace “fatan an samu Adnanu Ιin?” Girgiza kai Sarkin Ruwan yay yace “gaskiya babu wani labari, amma dai ga abinda muka samu” ya faΙa yana miΖawa Baffa rigar jikin Md Adnan karΙa Baffa yay yace “to mungode Ζwarai shi kuma Allah ya bayyana mana shi, idan yana raye ya kai sa hannu na gari” da Ameen Sarkin Ruwan ya amsa.
Har Baffa zai juya sai kuma ya nufi motar Akeem yana zaune zuwa lokaci ya zame rigar jikinsa daga shi sai singlet murΙaΙΙan Ζirjinsa ya bayyana, ga sumar nan har lokacin na zubda ruwa, banda sauke numfashi babu abinda yake.
“Mai sunan kawo” Baffa ya kira Akeem, gently ya Ιaga kansa tare da sauke ganinsa akan Baffa kallo guda yay masa ya Ιauke kansa yana taune leΙansa tare da lumshe gajiyayyun Maraitattun idanunsa.
“Nasan kana jin haushin na ne ko? Kana ganin kamar da gangan nai hakan ko, to wallahi tsananin son da nakewa yarinya ta yasa nai haka amma nama fika baΖin ciki a yanzu haka”
Shiru Akeem yana danna system Ιinsa ba zaka taΙa cewa dashi Baffa yake Magana ba, fuskarsa looking okay Babu wani sauyi.
Sanin halin Akeem yasa Baffa juyawa.
A tsaye Baffa ya samu Abbu yana kallon Akeela kafin yace “to ko dai kwana za kuyi ne?” Girgiza kai Abbu yay yace “A’a yanzu zamu tafi in sha Allah” da sauri Baffa yace “to bari na kwaso kayanta ko” kallon Baffa Abbu yay kafin yace “haba Baffa no need, Akeela is like my daughter zan mata komai” murmushi Baffa yay hawaye na saukar masa domin gani yake Ζanin nasa kawai daurewa yake rashin Md Adnan ba Ζaramin babban giΙi bane a rayuwarsa.
Baba Rabi ce ta shigo idanunta yay jaa sosai irin taci kuka ta Ζoshi, kafin ta kalli Abbu tace “Mungode sosai Alhaji Bukar Allah ya bayyana mana Adnanu cikin aminci” “Ameen” kawai Abbu yace domin sosai zuciyarsa ke masa zafi kuka ne kawai da bazai ba, amma ganin fuskar Akeela na yaye masa wani Ζuncin.
Baffa ya nufi wajan Akeela zai Ιauke ta da sauri Abbu yace “A’a Baffa, Ni da zamu tafi tare bari na Ιauke ta”
Hannu yasa ya Ιauke ta sassanyar Ajjiyar zuciya Abbu ya sauke yana jin zuciyarsa na sanyi sosai, wani mayataccen Murmushi Abbu yay tare da fakar idanun Baffa yay wani tura Ζasa tsakiyar wuyanta…
Bayan sallar magrib motocin su suka fara shigowa cikin haΙaΙΙan titin _Railway quarters Nasarawa, Kano_
A gida mai number 112 suka fara shigar da motocin bayan gatekeeper ya buΙe masu Ζaton gate Ιin.
Motar Abbu ce a farko shida Bala driver sai Akeela dake kwance a baya.
Mota ta biyu kuma P.a a ciki shi Ιaya yana janta motar Ζarshe kuma Oga Dr Abdul-hakeem Bukar Bello ne zaune ya Ιura hannunsa guda Ιaya a saman string motar Ιaya hannunsa kuma ya tsakiyar kansa yana hargitsa sumar kansa, a hankali kuma yake sauke ajjiyar zuciya ajajjere.
Zafi da raΙaΙi da zuciyarsa ke masa na tawowa da Akeela da Abbu yay yafi komai baΖanta masa, cos she’s the reason behind anything daya samu Md Adnan.
Bama ya so ya buΙe ido yaga yarinyar shiyasa yau zamansa cikin motar tare da lumshe idanunsa yana so Abbu ya shige da ita domin ta riga data zame masa mujiya.
A hankali Abbu ya buΙe back seat tare da zura kansa cikin motar, dim! dim!! dim!! Haka zuciyarsa ke bugawa aduk sanda ya kalli Ζyakkyawar fuskarta wata nutsuwa ta saukar masa.
Zama yay cikin motar tare da miΖa hannunsa gaba Ιaya biyun ya jawota sosai very close to him, hannunsa dake rawa yasa tare da yin baya da gashin ta wanda ya sauke wai wist Ιinta,
Lumshe idanunsa yay cikin Ζasa da Murya yace “Uhm baby na mai kyau, nine ko?” Ya faΙa yana shafa kanta sai kuma ya cireta sama tare da fito da ita daga cikin motar, dai-dai kunnanta kamar wacce ta kejin sa yace.
“I’m your dad, your boyfriend uhm baby kina cin abinci kuwa? You are so light Baby” ya faΙa yana tafiya da ita kamar wani mai sabon jini bayan yay jika da ita.
P.a dake tsaye ya Ιauke idanunsa a hankali kuma yabi bayan Abbu da some things na Md Adnan.
Tsayawa Abbu yay tare da danna wani ma danni a hankali Ζofar ya fara ja baya tare da buΙewa ciki ya shiga babban Parlo ne daga cikin Ζofar, iya haΙuwa ya haΙu komai na Parlo Ash ne daga kujeru zuwa Flowers da labulaye anything dai.
Ga Ζatuwar cineme kusan rabin bango sai deep frizer mai gida wajan uku,ga senter table a tsakiyar mai Ιauke da wata Ζatuwar flower jikin bangon parlon duk Album Ιin ayatul kursiyu ne, da fatha e.t.c
Daga can bayansa yaji ana faΙin.
“Ya..yah kamar dai Ζ΄an gudun hijira kuka faΙo mana gida babu ko Sallama? A’a babu ruwana kuda Allah tun dai duk musulmai ne a gidan da haka nan kamar Ζ΄aΖ΄an arna zaku faΙu mana gida, ai ko Ζ΄an dama ne ku kwayi sallama musan da zuwanku kuma musan abinda zamu baku”
Kallon Didi Abbu yay kafin yace.
“Afuwa Didi”
TaΙe baki tayi kafin tace “A’a astagafirullah mene kuma afuwa fisabilillahi kamar dai nace akan Bukari siya min tsire? A’a ni rayuwar duniya mai sauΖi na Ιauke ta, Wacece wannan kuma Aljanu take ko shan Inna ce ta kamata”
Ta faΙa Idanunta akan Akeela wacce take jikin Abbu.
P.a Murmushi Yay domin yana son dramer tsohuwar kafin yace.
“Barka da dare Didi”
Washe baki Didi tayi tace “A’a Ζasimu ince dai ka samu matar aure? Yooo ba Gwamma kai ba ko babu komai zan baka shawara mai kyau kabi, kaga dai babu dangi iya babu na baba jinΖai da tausayi irin nawa nasa aka baka aiki gashi kuma yanzu nace kaje wajan yarinyar idan ubanta har yanzu yaΖi yadda ta Aure ka kawai kayi mata ciki kaga ko babu komai dole a baka ita ka aura ni wallahi yarinyar ba tayi min ba” shi dai Shiru kawai yay yana Murmushi ita a dole shawara ta bashi idan kuwa haka ake bada shawara da an shiga uku.
Kwantar da Akeela Abbu yay a hankali kuma fara faΙin.
“Ummi!! Mami!!”
Mami ce ta fara fitowa idanunta ya kumbura sosai saboda kuka, baΖa kana ganinta kaga mahaifiyarsa Md Adnan zatai shekaru wajan 42 tana sanye cikin wani haΙaΙΙan lace, Zama tayi a kujerar dake farcing Abbu ba tare da tace komai ba.
Not too long Ummi ta fito daga part Ιinta hannunta riΖe da wata Ζyakkyawar Yarinyar zatai shekaru 4 haka fara ce sosai kamanin Akeem zane raΙau a saman fuskarta Amani kenan jika a wajan Alhj Bukar Bello Ζ΄ar kuma wajan Dr Abdul-hakeem Bukar Bello.
Zama Ummi tayi kusa da Mami tana sanye cikin wata orange Ιin lafaya tai mata kyau sosai zatai shekara 45 haka amma jikinta a murje yake sosai har tafi Mami gogewa da kuma wayewa.
“Barka da dare ya hanya” Ummi ta faΙa murya Ζasa.
Kallon su duk yay kafin fuska a Ιan haΙe domin bai fiya sakin fuska ba idan ba keΙewa yay da matansa ba yace.
“Kunga abinda ya faru da Adnan ko? Jikina yana bani yana raye kuma komai jimawa zai dawo gare mu, i believe cewa komai sai Ubangiji ya tsara mu Ιauki hakan a wata sabuwar Ζaddara daga Allah wacce ya jarabce mu domin gwada imanin mu, ko yarda na yarda cewa hakan ya faru ne dalilin shigarsa ruwan, amma ruwan ne dai kawai ya zama sanadi amma tuntuni Ubangijin AL-ARSHI ya tsara faruwar hakan a Lauhil Mahfouz…”
Da sauri Didi tace.
“SadaΖallahul Azeem,amma dai Bukari ka cuce mu da baka zama malami ba ka rasa mai zakai sai siyasa, ai yasin naji daΙi daka sauka daga kujerar mulkin baki Ιaya, ai da wallahi har govmet hausi Ιin zani nace bada yawo na ni Uwarka idan suka zaΙe maka, haka kurum na fita waje a dinga shunani da baki ana gata can Ιan ta yana handime kuΙin jama’a”
Ta faΙa tana cuna baki gaba, shi dai Abbu bai ce komai ba domin yasan rikicin tsofa ne.
“To! Ubangiji ya dubi idanun mu ya sanya Adnan yana raye ya kuma dawo gare mu, Allah ka dubi halin da muke ciki”
A sanyaye Mami tace “Ameen” idanunta na Ζara kawo ruwa ajjiyar zuciya Abbu ya sauke kafin ya kalli Akeela yace.
“Ζiyar Baffa ce da Baba Rabi dalilinta Adnan ya faΙa ruwan kuma Thank God Dr ya ciro ta…”
A nan ya kwashe labarin kakaf abinda ya faru ya basu.
Ihu da kuuu Didi tasa zani na faΙuwa tace.
“Kun kashe min Adnanu wallahi hisba zan kaiku”
Tana faΙin hakan ta nufi waje a hanya taci karo da Akeem dake shigowa fuska ya haΙe sosai ko alamun annuri babu.
Ganin haka yasa Didi washe baki tace.
“Yooo yanzu naji bayani ai cewa nayi bari na leΖa naji mai gidan Shiru fa”
Bai Ζara kallon ta ya matsa can gefe sallama ma ciki yay kai tsaye upstairs ya nufa wajan part Ιinsa.
Ganin haka yasa Abbu faΙin “Dr kazo ka duba Akeela” jin sunanta yasa Akeem yaji kansa ya sara Mami kam MiΖewa tayi domin tunda taji a kanta Adnan ya faΙa ruwa taji wata muguwar tsanarta ya cika Zuciyarta.
Da Ιan sauri Akeem ya Ζarasa haurawa saman ko takan Abbu bai bi ba ganin hakan yasa Ummi faΙin.
“Bari na duba ta”
Ζaukan ta Abbu yay zuwa part Ιin yaransa mata, Ιakin duhu alamar duk sunyi bacci On yay na wutar bedroom Ιin Aleema,Afaf duk suna kwance wajan Ameera da take zuwa hutu ya kwantar da ita, lokacin tuni Ummi ta Ιauko kayan aiki, cikin sauri ta fara duba ta ganin har yanzu da ruwa a cikinta yasa ta danna cikin da sauri sai ga ruwa na fita.
Tana Ζara dannawa Akeela tai hau yin tari.
Wata Ζoyayyiyar Ajjiyar zuciya Abbu ya sauke tana gama tarin kuma bacci ya Ιauke ta, sai da Ummi tayi mata injection kana ta Ιaura mata drip Abbu yi yayi kamar bazai fita ba ganin kallon da Ummi ke masa yasa ya Ιan shafa kansa yace.
“Miss You dear, let’s go”
Gaba yay ta bisa a baya kana ta jawo masu Ζofa,
Daman p.a tuni yay masu sallama ya tafi gida.
A hankali bakinsa ke motsawa yana tasbihi can Ζasa zuciyarsa, saboda zafin da zuciyarsa ke masa, cikin haΙaΙΙan parlonsa ya shiga komai na Parlon white ne.
Ya haΙu sosai har ba’a magana, kai tsaye wata corridor ya bi hadle Ιin Ζofar ya buΙe, wani irin lumshe idanunsa yay tare da sauke wani maraitaccen numfashi yaja tare da saukewa, saboda wani sassanyan Ζamshi daya daki hancinsa ya sashi lumshe idanun da bai niyya ba.
Tura kansa cikin bedroom yay bakinsa Ιauke da wata kamilalliyar sallama yana maida Ζofar ya rufe.
Derect bathroom ya nufa yana mai zare kayan jikinsa, a saman hanger ya saΖale tare da sakarwa kansa shower, a hankali yake sauke ajjiyar zuciya yana jin yadda ruwan yake dukan saman fresh skin Ιinsa.
Bayan yay wankan ya Ιaura alwala kana ta Ιauki wani long white towel ya dauraia wist Ιinsa, ko kansa bai tsane ba ya fito ruwa na sauka daga sumar kansa zuwa Ζwantaccen gashin Ζirjinsa.
Wani irin Ιaci bakinsa yake masa rabon da yaci abinci har ya manta wajan fridge ya nufa ya Ιauki Apple da cake ya fara ci bai wani ci da yawa ba ya ajjiye.
Wasu haΙaΙΙun nightwear slik Pajamas milk colour, a hankali ya miΖe tare da goya hannunsa a bayansa ya Ιan fara tafiya yana mai karanta addu’a yana bin duk kusurwa Ιakin da tofi bayan ya gama ya kwanta saman bed Ιin tare da jan duvet ya rufe jikinsa, gaba Ιaya ya Ζasa bacci tunda matarsa ta rasu wajan haihuwar Amani baya iya cikakken bacci ya saba da jikin mace sosai duk da auran kamar na dole ne bai so amma ya saba da jikin matarsa ainun.
A haka bacci ya Ιauke sa.
Misalin 4 na dare ta shiga buΙe idanunta wanda sukai mata nauyi kanta na sarawa sosai, hannunta mai Ιauke da carnoner ta kala Ιan marai-raice fuska tayi kamar wata Ζ΄ar baby Wanda ya sanya manyan dimples Ιinsa bala’in lomawa.
A hankali kuma ta shiga bin bedroom Ιin da kallo sosai gabanta ya faΙi ganin bata dan Ιakin ba, jiki babu Ζauri ta miΖe tsaye tana MiΖewa gashinta ta sauka har wajan manyan ass Ιinta.
Da Mamaki tabi jikinta da kallo ganin wata Robe Nightgown silver wacce ta sauka iya laps Ιinta gaba Ιaya manyan gwayen Ζafafuwanta suna waje ga wani gashi da yay kwance lub a saman fatar ta.
Shanyayyun idanunta wanda kullum suke a Lumshe ta Ζara buΙe, jikinta babu Ζwari ta nufi Ζofar data gani, tana tafe ko’ina na jikinta moving yake kamar tarwaΙa.
A hankali ta buΙe Ζofar ta fita ita bama ta san dare bane sai da ta fito parlon daga duhu ga wani masifafan sanyi na KaΙawa, da sauri ta matse jikinta waje guda ta shiga taune bakinta kamar wata Ζ΄ar turawa haka ta zama cikin nutsuwa take tafiya harta isa tsakiyar Parlo tana zuwa zata shige taji an sanya mata Ζafa baya tayi tare da hantsilawa zata faΙi wata kuma Ζyakkyawar Ajjiyar zuciya ta sauke jin ta faΙa saman Ζirjin mutum…
Post a Comment for "TSINTACCIYA CHAPTER 3 BY NIMCY LUV"