MAI TAFIYA CHAPTER 7 MAI TAFIYA CHAPTER 7 Www.bankinhausanovels.com.ng Ashe tsakanina da ke wani alamari ne mai ban mamaki? Ashe tsakanina da ke ‘yanuwantaka ce? Ashe tsakanina da ke soyayya ce? Me ya sa abubuwa ba sa zuwa a daidai lokacin da ya kamata su zo? Me ya sa su kan zo a kurarren lokaci? Me ya sa???? Almustapha Iliyaso Tillaberi7 ( you may need a tissue paper, this is going to be a tough ride. Going on a break i have exams to write. Do not conclude until you have read the last chapter, the last sentence, the last word. Few chapters to go inshallah)2 Hajiya Hadiza ke tafiya akan titin zoo road da ke kano. Tana hanyar zuwa wani biki diyar kawarta na nunawa sa’a. Nakasasshen mijinta ta bar shi a gida ko bi ta kan sa ba ta yi ba. Warin da ya isheta ne ma ya sa ta sa aka maida shi baskwata don ba zata iya ba.9 Kiri kiri abokiyar zamanta Khulsumou da ke Niamey ta ki zuwa sai faman aiken malamai ta ke. To ita ina za ta iya? Ta godewa Allah Almustapha dan ta shi ke kan komai da ina za ta sa…