BABBAR YARINYA CHAPTER 5 Oum Aphnan
BABBAR YARINYA CHAPTER 5 Oum Aphnan
Fuuu ta wuce Ιakinta ,taje kan hamshaΖin gadonta ta zauna tana dafe dakai tana faman girgiza ,kamar Ζ΄ar Ζwaya a dole an mata ba daidai ba,hajiya zainab da dunfarowarta kenan taga sanda ta kwalle bawan Allah da mari yasa Zuciyarta tsayawa da harbawa na wucin gadi,hakan ya baiwa Islam zarran wucewa safely .
Cikin Murya kamar za tayi kuka ta Ζarasa gaban Barrister Magan
“My Deepiest Apology onbehave of my daughter don Allah kayi haΖury yarinya ce,kai mata uzuri Afwan ,Mu shiga daga ciki ko?”
Ζagowa yayi da idanuwarsa da suka rine sukayi jajir ya kalleta,sannan yayi wani irin dariyar yaΖe da yafi kuka ciwo
“Momy Islam bata sona,basai na shigo ba,Sai Anjima”
Da sauri ya juya ba tareda ya kalli kowa ba ,ya nufi motarsa
“Suwaiba”
Ta Ζwallawa Mai aikinsu kira cikin tsananin fusata
Yarinyar kamar zata kifa ta zo gabanta cikin uniform Ιinta
“Na’am Hajiya gani!”
“Maza Jeki ,ki kiramun Islam,ko me takeyi tazo ina neman ta”
Dasauri ta juya ,zuwa Ιakin ,saidai tana cuna kanta tun kafin tayi magana ta jefeta da wani irin tsawa da ya sakata firgita
“Outttttttt!”
Da gudu suwaiba ta fita,itakuma Islam ta dafe maΖoshi tanajin yanda ke mata suya saboda Shouting Ιin da tayi.
Hajiya zainab da ta kira Akram a waya ,jan baya tayi akan kujera ta zauna a falon tana jijjiga Ζafa Ιaya duniyar nan kaf ta rasa meke mata daΙi ,tabbas Abun Islam ya fara wuce limit Ιin da za’ayi shiru ,this is not the first time da tayi wannan Abun,Alhaji buba kam Hankalinsa kwance ya ajiye katuwa pot belly Ιinshi sai gudanar da Sha’anin Business Ιinsa da jama’a yike ,sam kamar ma abunda Islam tayi bai damesa ba
Hajiya zainab zuru tayi masa da ido tana kallonsa ,cikin Ιacin rai,Yina faman waya Abunsa yina ΙaΙΙaka dariya
Shiru tayi dafe da tagumi har ya gama kafin ta Ιago ta kallesa
“Sweet Bakaji Abunda nace maka Islam tayi bane wai yau a cikin gidan nan?”
“Naji mana ,To me kikeso Inyi bacin ke kinba yaro haΖuri ,kuma nima nace maki anjima zamuyi waya sa me girma gomna,Don Allah kar mu daΖile rayuwar Ζ΄annan,tana iya yuwuwa rawar kai ya kawo mata irin na Ζ΄aΖ΄an masu Ζasa,itakuma ta nuna masa izzarta a sarari ,tunda ai inda itaΙin ba Ιiyar Alhaji Buba bane,Shima cewa zaiyi yafi Ζarfinta ,to shi Barristern mangan shiya jawa kansa daya Ιakko dala ba gamo”
Sakin hanci da baki tayi tana kallonsa ,har ya kai aya
“Oh really? Alhaji yarinyar nan a laifin da tayi har kana da bakin tare mata ,bama mu taru muyi punishing Ιinta ba?”
“Ah haba dai horo? Uhmuhmahah sam bashi yuwuwa inda Ace Ζ΄arnan Ζ΄an mitsiyata ne kare bazai tako hanyarta ba,kaf Ιinsu ribibinta suke saboda ita kaΙai Allah yaban ga dukiya na tara na sakar mata tai wadaΖarta dashi”
CaΙe baki kurum tayi ,ta juya kai daidai nan Akram ya shigo.
Cikin Nutsuwarsa ya ΙuΖa Ζasan kafet ya suka gaisa ,kafin Alhaji buba ya umurcesa da ya miΖe ya zauna a kan Kujeran.
Cikin Narkakiyyar murya wanda daga gani kasan tana cikin tsananin damuwa ta fara koro masa labarin abunda ya faru tsakanin Islam da Manga
Wani gauran numfashi yaja ya aje ,adaidai sanda yaji ta kai Ζarshen maganarta
“To ynx momy me kike ganin mafita ma wannan Alamarin don ni zahirin magana ,kaina ya kulle?”
Waigawa tayi ta kalli Alhaji buba da yayi kasaΖe ba tareda yace komai ba
“Alhaji kayi shiru meye mafita?”
“Karku damu dani hajiya zainab ,duk yanda kuka yanke ai Islam ikon ku ce”
Jan dogon Numfashi tayi “Shikenan ,to ni Abunda na yanke a raina shine ,a aurar da Islam shine kaΙai mafita,kuma aure cikin gajeran lokaci in ma so samu ne a yau Ιin nan inyaso tarewa sai bayan ta dawo daga UK”
Tsit Ιakin yayi ba wanda yace Ζala ,har sai da ta gaji tace” ya naji duk kunyi shiru ne ?”
“Hajiya zainab maganar ne yayi mun banbaraΖwai ,tunda nasan dai kinsan Islam batada wani manemi tsayayye duk korasu take”
Kai tsaye tai magana ba tareda ta kalli kowa ba “Oh baga Akram ba ,sai ai masu auren zumunta ,inta kama a yau yau Ιin nan !”
Da sauri akram ya miΖe tsaye bakinsa na motsi ya kasa magana,itama kuwa daidai ta sako Ζafa zatashigo taji furcin Hajiya zainab na Ζarshe
A gigice ta Ζarasa shigowa
“Auren zumunci? Nine zaaiwa auren dole sai kace wata Gantalalliya da tayi abun kunya,Abba dan Ιina kanajin matarka ? Hmm wait bari inji me zakace ,zaka biye mata ne ku aurar sani ga wannan abar (Ta yarfe hannunta tana nuna Akram from head to toe cikin mugun harara) ko kuma zaka biyewa raayin matarka ne,wacce na lura sam ta tsaneni baΖin ciki take mun”
Ζau! Ya yanke ta da mari ,dafe wajen tayi da sauri cikin mamaki tace “Ka mare ni,ehem mugu Azzalumi ? Wallahi sai kasan ka mareni kuwa ….Amaka!?” ta Ιaga murya tana kiran guard Ιinta
“In baki iya bakinki ba next time ni da kaina zan Ιauki dorina insa ya zane mun ke,shashasha kawai ,samu waje ZAUNA!! ….Akram Ιauki waya ka kiramun soba kabani in gayyace su Ιaurin Auran Islamiyya gobe da safe Inshaallah”
Post a Comment for "BABBAR YARINYA CHAPTER 5 Oum Aphnan"