ZURI'A DAYA BOOK 3 CHAPTER 4 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI'A DAYA BOOK 3 CHAPTER 4 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 4 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng Mun tsaya Ita kuwa Rauda abin da ta fuskanta shi ne, tsabar kishi ne ya fito Karara a tare da shi, to amma kuma ganin itama bai barta ba sai take tunanin kishin dai kawai ya fi nunawa a kansu. Www.bankinhausanovels.com.ng Take kuma wata zuciyar ta fada mata cewa kishin Haana ya ke yi, kawai dai ya yi miki haka ne don kar ki fahimci ya fi baiwa Haana kulawa ne. Dole ta hadiye wani abu da ta ji ya taso mata a can Kasan zuciyarta. A Bangaren Haana kuma, ta Kudire a ranta, daga wannan rana babu abin da zai sa ta sake zuwa wajen nan balle kuma ta dauko wa kanta damuwa irin wannan, duk kuwa son da ta ke . yiwa wasan. ‘ Haka kawai sai ta ji ta tsani wajen, ba ma ta sha’awarsa ko kadan yanzu. Duk yadda ta yi ta Boyewa Sameer damuwarta, sai da ya gane ta, don sau biyu yana neman da su je wajen, sai kawai ta ce masa kanta ne ya ke ciwo, haka zai ja su Rauda su tafi, har sai da aka gama wasan suka yi nasara a Karshen…