ZURI'A DAYA BOOK 3 CHAPTER 19 KARSHE BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI'A DAYA BOOK 3 CHAPTER 19 KARSHE BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 19 KARSHE BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng ta dauke ni mai son kansa da kuma rashin tausaya mata kan halin da ta ke ciki. Nasan ba za ta ki abin da ku ka sanyata ba, sai dai za’a tauye mata hakkinta na aura mata wanda bashi ta ke soba. Ni kuma Www.bankinhausanovels.com.ng burina naga ta samu farin ciki dauwamamme a cikin rayuwarta, don Allah Abba ku fahimci manufata, ba wai kawai son raina ne na ki amincewa da abin da ku ke so ba sai dai don ni din ni kadai ne abokin shawarar Amminka, ba don sanin abin da ta ke so ba da tuni na amince kun yanke hukuncin komai. Don haka Abba ina rokonka da ka bar Amminka ta auri wanda ta ke sO, ni kuma ka nemo min duk wacce ka ga ta dace da ni don kasan cewar ba ni da wani zabi da ya wuce naku, kuma wallahi zan riketa tsakani da Allah. ba za ka sameni da saba muku ba, fatana dai na ga Haana ta na cikin farin ciki. Jikin Abba ya yi sanyi, nan take ya ji ya sauke duk makamansa da duk wani fishi da ya ke dauke da shi na Abban, …