ZURI'A DAYA BOOK 3 CHAPTER 13 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI'A DAYA BOOK 3 CHAPTER 13 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 13 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng  Sarai Ya Abba ya fuskanci ba ta ji dadin abin da ya yi mata ba, amma shi cikin ransa ya ji dadin haka, don ya yi hakan ne don daya daga cikinsu ya Ji haushi, sai ya ga kamar damuwar tata ta fi ta Sameer. Nan da nan ji ya yi damuwa tana ziyartar zuciyarsa don kO kadan bai san ganın Haana dinsa cikin damuwa ko da kuwa wacce iri ce. Tabbas da ya san za ta shiga wannan damuwar da bai yarda sun tsaya ba.  Www.bankinhausanovels.com.ng Ya Abba ya yi saurin taka motarsa don su yi sauri barin gurin. Shiru motar ta yi babu wanda ya ce kanzal can dai Rauda ta ce,Sister wai mai ya faru da ku ke da Ya Sameer. Me ki ka gani kin san halinsa ba sai na fada miki ba. “Gaskiya ne. Yana jin su bai ce musu komai ba don bai son su sak0 masa maganar Sameer don ya ji ya bata masa rai domin shi ne ya janyo damuwar da ya gani a kan fuskar Haana dinsa nan ya ji yana son korar damuwar da take son zama a cikin ranta. Da sauri ya ce, Haana wai ina batun …