ZUMA CHAPTER 7 BY SHATUUU

ZUMA CHAPTER 7 BY SHATUUU
ZUMA CHAPTER 7 BY SHATUUU Www.bankinhausanovels.com.ng  Daddy ya cigaba da kwada ma yaya Mariya kira, hankalin shi a mummunan tashe ya mike tareda riko hannuna ya fito yana sake kiran yaya Mariya, da ace bamu tada generator ba babu abinda zai hana makwabta jiyo muryar Daddy.+ “Nawwara! Amina!! Amal!!!” Kusan dukka a tare suka fito kowacce sanye da kayan bacci, alamu sun nuna basu masan a yadda suka fito ba, dan kayan baccin mu yadda kuka san dakin miji zamuje, kanshi ya dauke daidai fitowar baba Asabe tana fadin “Baban Nanah lafiya? Me…” Se tayi shiru ganina a halin da nake ciki, sauran sunyi shiru kowa tunani yake me ya sameni haka? Sun san lafiya nake zaune Ummu ta kirani akan naje Daddy yana kirana, to me ya canja ni lokaci daya haka. “Asabe zanje zan kai Nanah asibiti, zamuje da Nawwara da Aminatu. Ki zauna da sauran” Bai ma jira me zasu ce ba yaja hannuna muka tafi, Nawwara da Aminatu suka zumbulo hijab suka biyo bayan mu, driver na ganin Daddy ya taso amma Daddy ya daga masa hannu, da k…