ZUMA CHAPTER 4 BY SHATUUU

ZUMA CHAPTER 4 BY SHATUUU
ZUMA CHAPTER 4 BY SHATUUU Www.bankinhausanovels.com.ng  Fitowar mu kenan daga lectures misalin sha daya, gaba daya nayi zuru zuru saboda yunwar da nake ji, ko dan tea din da nake sha ma yau ban sha ba saboda sauri na kusan makara. Hibba dake gefena tace+ “Nifa Allah ya isa ce kawai zata raba mu da mutuminnan, yasa muzo sannan yaki zuwa kuma ya hana fita” Tsaki nayi dan gwara ita tana jin karfin magana nikam I’m drained ji nake kamar hajijiya zata kada ni. Tare muka je wani eatery nan cikin school, banma jira menu ba na nufi counter din nayi placing mana order. Babu jimawa aka kawo mana seda nasha lipton din sannan na fara cin fried yam da sauce. Saboda dadi har rufe idona nake, seda muka gama tas mukai settling bill sannan muka fita. Dake se hudu mukeda wani lecture din yasa muka tafi hostel. Muna zuwa Hibba ta cire kayan jikin ta ta dauki zani ta daura tareda yin daidai a gadon. Zuwa nayi bayan na rage kayan jikina nace “Kiga yadda kika kwanta kamar wata giwa dallah can!” Dariya tayi ta ma…