ZUMA CHAPTER 3 BY SHATUUU ZUMA CHAPTER 3 BY SHATUUU Www.bankinhausanovels.com.ng Saura sati biyu na tafi kano, ranar Saturday Daddy na gida bai je ko ina ba, da safe ne ma brothers dinsa Kawu Lawan da Kawu Babandi suka zo daga hadejia mu muna bacci ma se da baba Asabe tazo ta tashe ni sannna naje muka gaisa na daura musu tea sannan nayi pepper soup na kaza. Misalin karfe biyu aka dawo da nepa wadda tun dare suka dauke, tashi mukai muka kwashe carpet din da muka baza a terrace din gaban parlon mu saboda zafi ake bana wasa ba. Zama mukai muka fara kallo kamar yadda muka saba, mikewa nayi naje na hadawa Hudayyan Mom cereals na janyo ta jikina ina feeding dinta, yaye aka kawo mana ita, tana shan gata a gurin mu and I’m sure idan ta koma gun iyayenta zasu ce mun bata musu yarinya. To ya zamuyi duk cikin mu babu wanda bai iya raino ba, idan Hudayya ta tashi tana kuka cikin dare to dukkan mu se mun tashi mu kafa lallashi.+ Seda ta koshi sannan na goya ta a bayana tayi luf tareda fara bacci. Zama nayi se muka ji sallama…