ZUMA CHAPTER 2 BY SHATUUU ZUMA CHAPTER 2 BY SHATUUU Www.bankinhausanovels.com.ng Inajin tamkar na tafi kawai na fada muku wanene Aliyu cikin rayuwa ta amma se naga zaifi muhimmanci idan na baku labarin daki daki. Dukkan mu munyi tunanin Daddy zai hakura kamar yadda ya saba, amma wannan karan shima se ya kyale mu, ya daina shiga harkar mu kai tamkar bai san me muke yi ba, hakan ba karamin tayar min da hankali yayi ba, saboda hakan na nufin ba zanje FUD din ba. Seda mukai kwana uku a haka sannan a rana ta hudu duk suna bacci na fito na nufi parlon shi, dake Saturday ce nasan dama babu inda zaije, ile kuwan yana zaune yana waya, language din da yake using ya tabbatar min da yan uwansa lawyers yake magana, zama nayi a cushion din dake facing dinshi time to time muna hada ido dashi se inyi saurin dauke nawa idon, idan kuma muka hada se na marairaice kamar zanyi kuka, bayan wajen mintina talatin yayi hanging wayar tareda kallona yace+ “Nanah! Ya akai?” Langwabar da kaina nayi nace “Daddy good morning” “Morning sweetheart…