ZABI NA CHAPTER 9 BY FADEELARH ZABI NA CHAPTER 9 BY FADEELARH Www.bankinhausanovels.com.ng GIDAN MALAM FAROUQ ABDALLAH MALALI+ Zaune suke a falon gidan yayinda suka yi tsit suna sauraron Abba wanda ran shi yake a bace.. kukan yaran kawai kake ji.. na Layla kuwa harda shesheka. “Dukkanin ku kun sani cewar a nan falon na tara ku akan maganar yaron nan Zayd.. idan ban manta ke Layla da bakin ki kika ce baki son shi sannan a gaban ki aka yi maganar yace yana son qanwar ki Ameera.. Me zai sa yanzu ana maganar saura ‘yan kwanaki ayi bikin su zaki kawo maganar banza irin wannan??” Cikin kuka Layla tace “Abba na sani cewar nace bana son shi a baya amma wallahi yanzu ina son shi kuma ni shi zan aura..” ta nuna Ameera tace “duk laifin munafukar nan ne, ta sani cewar Zayd mai kudi ne shine bata fadi mun ba.. tana kallo na rabu da shi shine ita ta zagaya ta..”3 “kiyi mun shiru anan wurin.. Sakaryar yarinya. Ashe kina cikin masu kwadayi da son abun duniya kenan?? Mu qaddara dagaske Zayd din mai arziki ne, kenan saboda hakan zaki aure…