ZABI NA CHAPTER 13 BY FADEELARH

ZABI NA CHAPTER 13 BY FADEELARH
ZABI NA CHAPTER 13 BY FADEELARH Www.bankinhausanovels.com.ng  Washegari!!+ ZAYD AHMAD FADOUL’S RESIDENCE UNGUWAN RIMI GRA Kwance take a kan gadon dakin shi wuraren qarfe Goma da rabi na safe tana bacci.. wayarta da take ringing (Video call) ce ta tashe ta daga baccin.. Ko da ta duba gani nayi tayi murmushi yayinda ta gyara kwanciyarta tayi answering.. A yau din dai tun da safe Zayd ya tafi ofis a dalilin zai yi wani brief meeting da wasu clients da suka zo daga Sokoto.. Shi ya hada musu breakfast suka ci sannan ya wuce.. Gaba daya ya shagwaba Ameera, komai shine yake yi mata. Bai bar gidan ba sai da ya tabbatar ta koma kan gado ta kwanta don ta samu enough sleep and rest.2 Wuraren qarfe tara da rabi suka gama meeting din a nan office dinshi ya sallame su.. tun daga nan kuwa ya kasa yin komai.. gaba daya tunanin shi ya koma kan Ameera. A rayuwar shi bai taba sa ran mace zata birkita mishi qwalwa ba haka, bai taba sa ran akwai lokacin da zai ji baya iya yin aikin shi da yake so with passion ba …