YAR MAHAUKACIYA CHAPTER B KARSHE BY SAJIDA YAR MAHAUKACIYA CHAPTER B KARSHE BY SAJIDA Www.bankinhausanovels.com.ng Sun jima zaune sunyi shiru kowa da abinda yake sakawa a zuciyarsa jiran vilowar Elhaj Muhammad suke , Bayan kamar minti arba’in sai gashi ya shigo da damin goro a hanunsa yayi salama Suka amsa masa a tare suna kalonsa Waje ya samu ya zauna ya fuskance su ya ce ” cikin ikon Allah an daura aure a gaban shedu sanan kuma ga goro na samu Kiran sarki na shaida masa ya ce eh aure taya shi ake Allah ya sanya alkhairi, Hajiya Hawau ta ce” kana nufin *Rahma* ta zama matar *Dan Aljannah*? Elhaj Muhammad ya ce ” Kwarai kuwa ni na wakilce ta liman ishak ya wakilci Mubasshir Allah ya sa alkhairi aka hada Hajiya Hawau ta ce ” Alhamdulilah Allah abin godiya tabas alkhairi aka hada Allah ubangiji ya fi karfin su Allah ya kare duk wani mugun abin da za’a jefa dan a bata wanan taraya sanan Allah ya hada Hankalinsu Hajiya Fadimatu ta amsa da Amin ya Allah Haka suka gama suka tatara suka nufi gidan Hajiya fadimatu Suna shiga suka tarar da Yar M…