WALIJAAM CHAPTER 8 BY MAMAN TEDDY

WALIJAAM CHAPTER 8 BY MAMAN TEDDY
WALIJAAM CHAPTER 8 BY MAMAN TEDDY Www.bankinhausanovels.com.ng  “Koda ya isa barrack din gidan shi ya nufa ,tsawon kwana biyu baya da walwala sai dai kaman yanda yayi mawa mahaifin nashi alkawari bai sa6a masa ba domun kuwa tun ranan da ya sauka yasa aka fara sauya masa komai na gidan , Sam su Sadeq basu damu da ganin wannan sauyin yanayin daga gareshi ba don dama sun dade da sanin halin Anwar din ,sai ya kwana ya wuni bai ce mawa kowa komai ba indai ba kaine ka tanka shi ba, wannan kadanne na daga miskilancin Anwar . Zaune duka suke kowa na abun da ya saba ,shi Sadeeq na can yana fira da mata Yayin da Anwar ke sana’ar sa Shikam Abbas sai wani murmushin nishadi yake yi don yau gurun shi ya cika ,ya jiyo labarin inda wannan yar fulanin take da zama ,a yanxu abu daya ya rage masa shine tayanda zasu na haduwa da ita . Abbas lafiya sai wani murmushi kakeyi kana fara’a sai kace an maka albishir da gidan Aljjana?. Cewan Sadeeq yana mai datse wayan tashi hadi da kallon Abbas da har wannan lokaci…