UMM ADIYYAH CHAPTER 66 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 66 BY AZIZA IDRIS GOMBE
UMM ADIYYAH CHAPTER 66 BY AZIZA IDRIS GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  Ban fahimci a matsayin wa ka ke min magana ba.” TJ ya fada lokacin da ya Kankance idanunsa. A matsayin Yayanta na ke fada maka, kar ma ka bari na fara akan matsayina na daya bangaren. Amma saboda adalci, zan fada maka ka shirya samun wasu tsaiko, ba ka tsammanin na bar maka ita haka kawai ko?” “Ina ga da ace akwai wani abu makamancin hakan da ba ma wannan maganar a yanzu, saboda ta kasance ta ka a wata gaba. Ka yi sake da damar ka. Ina ga ko ka tsaya ka ga iya yina ko kuma ka sameta, ta fada maka abinda ba ka sani ba.” Maganar ta kona Zaid ba na wasa ba, amma bai yi mamakin abin da ya ce ba, saboda a hakikanin gaskiya shi ne ya yi sake da damar sa kamar yadda TJ Ya fada masa, amma shin ya shirya nade hannu ya sa masu idanu? A’a ba zai tsaya ba, har sai ya ga abinda ya turewa buzu nadi, zai kwato Twinkle dinsa! Wasu lokutan abu kalilan muke bukata da za su bude mana idanu su ingiza mu zuwa hanyar da ta dace, na yarda da cewa hakan…